Jami’an tsaro sun kama ’yan Najeriya 11 da suka yi wa turawa dafarar kudi kimanin Naira biliyan shida (Dala miliyan 5.7) ta hanyar soyayyar karya a kasar Jamus.
Hukumar ’yan sandan Jamus ta ce sama da mutane 450 ne aka yi wa irin wannan damfara a shekarar 2023 kadai, inda aka raba su da kudadensu kimanin Naira biliyan 5.8.
A ranar Laraba rundunar ’yan sandan yankin Bavaria ta sanar cewa, shekaru ’yan Najeriyan da aka kama 23 ne zuwa 59, kuma mambobin wata kungiya mai suna Black Axe ce.
An kuma gano cewa kungiyar Black Axe ta kware wajen fakewa da soyayya sauran dabaru wajen damfarar jama’a a kasashe daban-daban.
Kungiyar na fakewa ne da sunan kungiyar mai fafutar kare hakki a Afirka — sunan da ta amfani da shi wajen karbe kudaden da mambobinta suka damfari turawa.
Sauran ayyukan laifi da aka gano na kungiyar Black Axe sun hada da safarar dan Adam, karuwanci, safarar miyagun, kwayoyi, da kuma safarar kudaden haram.
Sun bayyana cewa masu damfarar suka yi basaja ne da sunayen bogi, a matsayin masoya ga Jamusawa; daga baya sai su fara amfani da dabaru iri-iri na neman ma’auran nasu su tura musu kudi.
Idan suka shawo kan masoyan nasu kan wannan bukata, sai su sa masoyan nasu su sayo kayan jinkai su aiko musu su zuwa Najeriya.