Malam Aminu Isa (ba sunan gaskiya ba ne) daya ne daga cikin mutanen da suka rabauta da tsarin auren zawarawa a zamanin tsohuwar gwamnatin Kano ta Rabi’u Musa Kwankwaso shekara 12 da suka gabata.
A tattaunawarsa da Aminiya, Aminu ya bayyana yadda zafin kishi ya sa amaryarsa ta rika samun sabani da matansa na gida, da kuma wofintar da lamarinsu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi ya sa auren ya mace.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Tarin Fuka Ya Yi Ƙamari A Kano
- CBN ya sha alwashin farfado da darajar naira a kasuwar canji
“Tun kafin mu yi auren zawarawa muka hadu da ita a Hisba inda nake aiki. Sai kuma Allah Ya kawo maganar auren zawarawa sai muka yi amfani da damar muka yi aure.
“Mun bi dukkan matakan da aka shirya kama daga na juna biyu da sauran larurori kamar yadda aka yi wa kowa. Mun yi aure lafiya har mun haifi ’ya’ya uku da ita.
“Amma shekara 5 ke nan ba ma tare, saboda rigima da suka yi da matana biyu na gida saboda kishi har da makami.
“Kin san mata da zafin kishi, wasu na iya dannewa, wasu ba sa iyawa. Wannan ne ya sa na ajiye ta na ba ta hutu.”
‘Idan na samu hali zan dawo da ita’
Malam Aminu ya ci gaba da cewa, “Amma dai ba mu rabu gaba daya ba, idan na samu dama zan iya dawo da ita.
“Kuma muna gaisawa muna wasa da dariya idan na je ganin ’ya’yana da ke wurinta.
“Yanayin rayuwa ne ma a yanzu ya sa ban dawo da ita ba saboda sai in biya sadaki in nema ma ta muhalli don gudun rigima.”
‘Abin da ya sa ake samun matsala’
Aminu ya ce watsi da tsarin auren da gwamnatin Abdullahi Ganduje da ta biyo baya ta yi ne ya sa auren ya kai ga rabuwa, domin kwamitocin da Gwamnatin Kwankwaso ta kafa a wancan lokaci don ganin hakan ba ta faru ba za su iya kawar da ita.
“Ina da yakinin da a ce gwamnatin da ta faro tsarin ta dore, to da lamarin bai lalace haka ba, saboda har kwamitin bibiya ta samar domin shiga tsakani idan matsala irin haka ta auku,” in ji shi.
‘Ina alfahari da auren’
Ya ce duk da wannan mishkila duk lokacin da ya kalli ’ya’yansu uku da suka haifa da ita, kara godiya yake ga Allah.
“Idan na kalle su na kuma tuna da ranar aurenmu, ina jin farin cikin da ba zan manta da shi ba. Domin suna karatu a makaranta sun samu tarbiyya,” in ji shi.
‘Mutane da dama da suka yi auren suna tare har yanzu’
Aminu ya ce, “Mutane da yawa sun ci gajiyar shirin kuma ya yi karko. Mun san da dama daga ciki. Wasu kuma kin san mata, idan ba a yi musu nasihohi da wa’azi ba, sai su ga kamar wata hanyar samun kudi ce ta zo musu.
“Da yawa su aka fi samu da haka a wurin tantancewa. Don akwai wadanda aka samu ana yin auren suka rabu da mazan saboda don kayan daki suka yi dama, amma wasu sun zauna.
“Akwai wani da ina wurin amma ban san sunansa ba ya kawo karar matar ta yaudare shi, kuma shi da gaske yake son ta. Bayan an yi auren ashe ita kayan dakin take bukata ana kwana biyu ta saka rigima da taratsi sai ya sake ta a karshe haka aka yi dole saboda ta hana shi natsuwa,” in ji shi.
‘Matar da na samu ’yar Aljanna ce’
Shi kuwa Is’hak Sani da aka fi sani da Baba Hedimasta ma’aikacin Hukumar Hisba cewa ya yi a tsawon shekara 13 da suka yi aure da tasa amaryar ya sa ya lakaba mata “‘Yar Aljanna.”
“Ba mu taba samun wata gagarumar matsala ba, sai ta yau da gobe da ba za a rasa ba a tsawon wannan lokaci.
“Mu dama can masoya ne da ke shirin aure ba wai sai da muka shiga tsarin muka hadu ba. Kasancewar ni ma’aikacin Hisba ne ya sa na ce to ga hanyar da za mu samu saukin abubuwa bari mu ci gajiyarta.
“A haka muka shiga tsarin muka tsallake duk wata tantancewa da ake yi har muka yi aure. ’Ya’yanmu 4 kuma duk suna nan lafiyarsu lau suna karatu. Kuma ba mu fuskanci wata matsala ba sai ma tagomashi da muka samu.
“Lokacin auren nan gwamnati ta yi mana gata. Ta ba mu kyautar shadda da sauran angwaye yadi 10 kowane mu dinka mu sa ranar auren. Mata kuma aka ba su jari aka kuma yi musu kayan daki.
“Jarin nan da aka ba ta har muka yi aure kuma tana sana’arta; tana dinka jakunkunan mata tana sayarwa, amma yanzu jarin ya dan kwanta saboda yanayin rayuwa, hidindimu sun yi yawa, ga shi ba mu da karfi,” in ji shi.
Sabanin Aminu, Baba Hedimasta ya ce nasa matan suna zaune lafiya da hadin kai, haka ma ’ya’yan da suka haifa.
“Asalin ’yar Aljanna da na ce miki ita ma ina fada mata, uwargidana na sanya wa har ya bi ta kowa ma ke kiranta da haka.
“Sai amaryar tawa ta ce ita ma na rika kiranta haka, sai na kada baki na ce saboda uwargida na kyautata min ne nake kiranta da haka, ke ma idan kina yi sai in saka miki, haka kuma aka yi,” in ji shi.
Muna nazarin auren baya don gano halin da suke ciki — Hisba
Hukumar Hisba ta ce yanzu haka tana bibiyar aurarrakin baya da gwamnati ta yi domin gano ire-iren wadannan matsaloli, ta kuma magance su.
Kakakin Hukumar, Malam Lawan Ibrahim Fagge ya bayyana wa Aminiya cewa Gwamnatin Kano a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ba hukumar damar yin haka ne, domin inganta wadanda za a yi a gaba.
“Akwai kwamitoci daban-daban da ake shirin kafawa wadanda za su bibiyi bayanan da muke da su na wadancan aurarrakin baya da muka yi.
“Da bayanan da muka tattaro za mu hada rahoto mu mika musu, su kuma su yi amfani da su domin daukar mataki na gaba da kuma tsara na gaba da yanzu gwamnatin ta ce za ta yi,” in ji shi.
Shawarwarin ma’auratan ga gwamnati
Dangane da ci gaba da auren da gwamnatin ta ce za ta yi, Hediamasta ya ce akwai bukatar ta bibiyi na baya da aka yi domin wasu da dama sun mutu, don gano dalili da yiwuwar farfado da su.
“Ko a wancan karon da muka yi na fada miki akwai abubuwan da aka samu na wadanda a wajen tatancewa aka gano suna dauke da juna biyu, kuma aka sallame su.
“Wasu kuma suka zo miji da mata ne amma suka hada baki suka zo cin kayan daki asirinsu ya tonu,” in ji Hedimasta.
Ga masu son cin gajiyar tsarin kuwa ya roke su da su ji tsoron Allah, su kuma duba niyyar gwamnati na son taimaka wa al’ummarta marasa karfi, kada su dakile wa masu niyya mai kyau damarsu.
Shi ma Malam Aminu ya ce shawararsa ga gwamnati ita ce ta rika jan kunne da kuma bayar da horo ga mata da mazan da za ta aurar a gaba kafin ta ba su jari.
“Dalilina na fadar haka shi ne wasu da aka ba su jarin cinyewa suka yi, amma idan aka ba su horo misali kuma ya zama kyautar keken dinki aka ba su, abin zai dore saboda ba kowa ne ya iya juya kudi ba,” in ji shi.