Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa.
Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
- Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara
- Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025.
Dawakin Tofa ya ce Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya fitar da sanarwar dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take.
Baya ga haka, gwamnatin ta umarci a rubuta takardar neman bahasi daga hadimin da aka dakatar, bisa kalamansa masu tsauri da suka shafi raɗe-raɗin shirin sauya sheƙa da ake zargin Kwankwaso zai yi.
Gwamnatin ta kuma ja kunnen dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da kada su riƙa fitar da bayanai ba tare da izini ba, tana mai jaddada cewa duk wata sanarwa daga gwamnati sai an tabbatar da ita kafin a bayyana ta ga jama’a.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da hannu cikin kalaman da Rabi’u Ibrahim ya fitar, tana mai cewa wannan magana tasa ce kawai, kuma ra’ayinsa ne shi kaɗai, bisa wasu dalilai da shi kaɗai ya bar wa kansa sani.
Sanarwar ta kuma tunatar da al’umma cewa, Kwamishinan Yaɗa labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Wayya, shi ne kaɗai ke da hurumin yin magana a madadin gwamnatin jihar.