✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kashe matashi a Kano

Mazauna unguwa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne.

Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe wani matashi a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe matashin ne mai suna Shuaibu Muhammad da adda, bayan sun shiga gidan da yake zaune da nufin sata.

Wani abokin kasuwancinsa, Haruna Nuhu Hussain, ya ce gungun ’yan fashin sun shigo gidan da suke zama a daidai lokacin da suke shirye-shiryen tafiya sallar Asuba.

To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.

Kimanin mutum 10 sun bayyana cewa ko a kwanakin nan jagoran ’yan fashin da aka kama ya yi wa wasu mazauna fashi da makami.

Ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.