Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta rufe wasu gidaje biyu da ke zaman ɗakunan kwanan ɗalibanta mata a Jihar Kano.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Hotoro da titin UDB a Kano saboda zargin rashin ɗa’a.
- Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa
- Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL
Wannan jami’i da ke kula da ɗakunan kwanan, Hamza Garba, ya ce an ɗauki matakin ne a ƙoƙarin da jami’ar take yi na tabbatar da aminci da tsaro da kuma daƙile duk wata kafa ta aikata masha’a a tsakanin ɗalibai.
Jami’ar ta ce cikin dalilan da ta ɗauki wannan mataki akwai ayyuka na rashin ɗa’a, ƙarancin ruwa da wutar lantarki, tashin-tashina da kuma tsugunar da waɗanda ba su cancanta ba a gidajen.
Sanarwar ta buƙaci ɗaliban da ke zama a gidajen biyu da su tattara komatsai da zarar sun kammala jarrabawar zangon farko.
Kazalika, sanarwar ta yi kira ga iyayen ɗaliban da cewa kada su zargi jami’ar kan duk abin da ya faru da ’ya’yansu da suka bijirewa wannan umarni.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a shekarar 2022 ce jami’ar ta Maryam Abacha ta samu lasisin soma gudanar da harkokin karatu amma har kawo yanzu ba ta tanadi ɗakunan kwanan ɗalibai a cikinta ba.
Sai dai jami’ar ta ƙulla yarjejeniya a hukumance da wasu masu gidaje da ke bayar da haya domin tsungunar da ɗalibanta.