✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano

Sai dai yayan budurwar ya bayyana nadamarsa yana mai ba da haƙuri ga duk ’yan uwan mamacin.

Rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da kama wani matashi bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa da ya wanke ƙafa ya tafi zance gidansu.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kiyawa ya bayyana cewa matashin ya fito da gora kuma ya buga wa saurayin da ya je zance gidansu a ƙauyen Kunya da ke Ƙaramar Hukumar Minjibir a Kano.

Sanarwar ’yan sandan ta ce matashin wanda ɗan asalin ƙauyen Goda, ya je Kunya ne wajen budurwarsa domin zance.

Sai dai jim kaɗan bayan zuwan nasa sai aka yi zargin cewa yayan budurwar mai suna Mansur Umar mai shekara 25 ya doke shi da sanda a ka, lamarin da ya haddasa masa munanan raunuka.

“An garzaya da shi asibitin Kunya daga baya kuma aka mayar da shi Asibitin Murtala domin ba shi kulawar gaggawa, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa,” a cewar Kiyawa.

’Yan sanda sun ce tuni suka kama Mansur, domin gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan jihar.

Rundunar ’yan sandan ta yi kira ga jama’a su riƙa sanya haƙuri a cikin al’amuransu, tare da kai rahoton duk wata jayayya da aka samu tsakanin wasu mutane zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Cikin wani sautin murya da Kiyawan ya sake wallafawa, matashin ya bayyana nadamarsa tare da neman afuwar duk makusantan mamacin.