✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya sha alwashin farfado da darajar naira a kasuwar canji

Tinubu ya damu sosai da abubuwan da ke faruwa a kasuwar canjin.

Babban Bankin Najeriya CBN ya sha alwashin bullo da sabbin matakai don magance faduwar darajar naira a kasuwar sauyin kudi.

Matakin na zuwa ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da Mukaddashin Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi a yau Litinin.

Da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Mista Shonubi ya ce Tinubu ya bayyana damuwa kan halin da kudin kasar ke ciki a kasuwar canji ta duniya, lamarin da ya ce zai yi aiki don magancewa.

“Shugaban Kasa ya damu sosai da abubuwan da ke faruwa a kasuwar canjin, ya nuna damuwa game da rayuwar talaka,” in ji shi.

Ya jaddada yakinin cewa nan da ’yan kwanaki masu zuwa za a ga kyakkyawan sauyi dangane da matakan da aka dauka.