✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace malami da jaririn da aka haifa masa a Kaduna

Maharan sun sace malamin da matarsa da 'ya'yansa guda biyu ciki har da jaririn kwana daya a duniya.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban malami, Malam Abubakar Musawy Ibrahim tare da matarsa ​​da ‘ya’yansa biyu a Jihar Kaduna.

An ruwaito cewa har da jaririn kwana daya a duniya suka sace a lokacin da suka kai harin a ranar Larabar makon jiya

‘Yan bindigar sun shiga gidan malamin da ke Karfi a Fondisho, unguwar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

A cewar majiyoyin yankin, an sace su ne kwana daya da haihuwar jaririn.

Wani makusancin malamin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa malamin shi ne shugaban kungiyar Hayatul Islamiyya ta Kawo da ke Kaduna.

“Shi da matarsa ​​da jaririn da ta haifa kwana daya, da kuma dansa, duk an sace su.

“Kawo yanzu dai ba a san inda suke ba. Kuma abin takaici ne shi ne yadda ‘yan bindigar ke neman kudin fansa har Naira miliyan 20,” in ji majiyar.

Majiyar ta koka da cewa iyalan wadanda abin ya shafa talakawa ne kuma ba za su iya tara kudin fansar da ake nema ba.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mansur Hassan, ya yi alkawarin yin karin haske da zarar ya samu cikakken bayani.