✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai da na shafe wata daya ina wanka da kokon kan mutum – Dan damfara ta intanet

Ya ce an ba shi lakanin ne da nufin samun sa'ar kasuwa

Wani dan damfarar intanet da aka fi sani da ‘Yahoo’ da aka kama a Jihar Ondo, ya ce sai da ya shafe tsawon wata daya yana wanka da kokon kan mutum don neman budi a harkokin shi.

Mutumin, mai suna Franklin Akinyosuyi, ya ce kuncin rayuwa ne ya tilasta shi nyin hakan.

Tun farko dai makwabtan mutumin ne suka kai karar shi bayan an tsinci kokon kan mutum da wasu kayan tsafi a gidan da yake haya, kafin daga bisani ’yan sanda su kama shi.

Da yake bayani ga ’yan jarida lokacin da aka yi bajekolinsu, ya ce wani kawunsa ne ya kai shi wajen wani boka domin ya samu karin budi a sana’arsa ta daukar hoto da sayar da kayan sawa.

Ya ce, “Bokan ya karbi Naira dubu 200 daga hannuna, inda ya hada min wani tsimi da ya ce na rika sha. Na biya shi kudina a cikin mako uku.

“Ya ce na rika wanka da kokon kan mutum da misalin karfe 1:00 na daren kowacce ranar Alhamis.

“Na yi hakan na tsawon wata daya, amma ban ga wani bambanci ba a harkokina. Hakan ne ya sa na kira shi na bukaci ya dawo min da kudina,” in ji shi.

Franklin ya ce ya kira bokan domin ya je ya dauki kokon kan, amma ya ki, kodayake ya amince zai biya shi kudin da ya karba.

“Daga nan ne na yanke shawarar jefar da kan, inda na jefar a bayan gidana. Sai dai an yi rashin sa’a, lokacin da na fita kafin na dawo, yaran mai gidan da nake haya sun gani, inda suka fada wa mahaifinsu, shi kuma ya kira ’yan sanda,” in ji Franklin.

A cewar Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, binciken da aka ’yan sanda suka dada yi a kan batun ya sa sun sami nasarar kama wani mutumin mai suna Dare Oyegoke, wanda ya yi ikirarin shi mai wa’azi ne.

Ta ce Dare din ne ya taimak wa Franklin da kokon kan mutum din, wanda ya ce ya samo shi ne daga wajen wani dan bijilan mai suna Asekun, mazaunin yankin Ikirun, da ke Jihar.