✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa

Gwamnatin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da Bazoum kan cin amanar ƙasa da kuma zagon ƙasa ga sha’anin tsaro

Gwamnatin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan zargin babban cin amana da kuma zagon ƙasa ga sha’anin tsaron ƙasar.

Masu juyin mulkin sun ce sun tattara hujjojin da za su yi amfani da su wajen gurfanar da Bazoum da kuma waɗanda suka kira muƙarrabansa na cikin gida da na ƙasashen waje.

Ministan Matasa da Wasanni, Kanar-Manjo Amadou Abdraman ya sanar a talabijin a ranar Lahadi cewa za su gurfanar da Bazoum da muƙarraban nasa ne a cikin ƙasar Nijar da kuma gaban hukumomin da suka dace na duniya, kan babban cin amanar ƙasa da yin zagon ƙasa ga tsaron Jamhuriyar Nijar.

Bazoum na cikin ƙoshin lafiya —Sojoji

Tun ranar 26 ga watan Yuli da sojojin suka yi wa Bazoum juyin mulki suke tsare da shi da matarsa da ɗansa a cikin gidansa.

Shugabannin sojojin na iƙirarin cewa ba mamaye gidan nasa suka yi ba, domin kuwa yana ci gaba da mu’amala da sauran duniya, kuma likitansa na zuwa ya duba shi a kai a kai, yadda ya saba yi.

Wani mashawarcin Bazoum ya tabbatar cewa a ranar Asabar likitan ya samu duba lafiyar hamɓararren shugaban ƙasar.

Sojojin sun ce, ”Likitan ya tabbatar cewa babu wata matsala a tattare da lafiyar Mista Bazoum da ta iyalinsa.”

An yi garkuwa da ni —Bazoum

Amma Bazoum ya yi zargin cewa sojojin sun yi garkuwa da shi ne, inda suka bar shi a cikin duhu, kuma babu abincin da suke ba shi, in banda gayar shinkafa da taliya.

‘Takunkumin ECOWAS haramtacce ne’

Sojojin na Nijar sun yi tir da takunkumin karya tattalin arziki da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba musu.

Sun bayyana cewa matakin haramtacce ne, baya ga kasancewarsa tsantsar rashin imani.

Masu juyin mulkin sun bayyana cewa matakin da ECOWAS ta ɗauka  ya hana ƙasarsu samun abinci da magunguna da kuma wutar lantarki.