✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanke Alaƙar Soji: Muna tattaunawa da Nijar — Amurka

Nijar ta kawo karshen alaƙar da suka ƙulla tun 2013.

Kasar Amurka ta ce tana tattaunawa da Shugabannin Mulkin Sojin Nijar, kan matakin da suka dauka na kawo karshen alaƙar soji da ke tsakanin kasashen biyu. 

Kakakin Ma’aikatar Kula da Harkokin Wajen Amurka, Matthew Miller, ya ce kasar na sane da matakin da gwamnatin sojin Nijar ta dauka.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), ya ce duk da daukar matakin da gwamnatin sojin Nijar ta yi, har yanzu Amurka na ci gaba da tattaunawa da su kuma nan gaba za su yi karin bayani kan lamarin.

A baya dai akwai alaka mai karfi tsakanin Amurka da Nijar, lamarin da ya sanya ta girke akalla sojojinta 1000 a kasar.

Nijar Ta Kawo Karshen Alaƙar Soji Da Ke Tsakaninsu

Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar karkashin shugabanta, Janar Abdourahamane Tchiani, ta soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.

Gwamnatin ta sanar da haka ne, bayan da ta soke irin wannan alaka tsakaninta da kasar Faransa.

Tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki ne a ranar 26 ga watan Yulin 2023, tare da hambarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Bazoum.

Amurka da Nijar sun kulla yarjejeniyar soji tun 2013, wadda a karkashinta dakarun Amurka da ke hamada suke amfani da kananan jiragen sama marasa matuka wajen yakar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Sanarwar na zuwa ne kwana daya, bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kammala ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku.

Tawagar ta tattauna da gwamnatin sojin kasar kan batutuwa da dama ciki har da kokarin kara kyautata alakar da sojojin ke yi da Rasha.

A cewar sanarwar da kakakin majalisar gwamnatin sojin Nijar, Kanar Amadou Abdramane ya karanto a gidan Talabijin din kasar, ta ce zaman da Amurka ke yi a kasar ya saba wa ka’idar doka da kuma tsarin dimokuradiyya na cin gashin kan kasa.

Sai dai tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a kasar, al’amura sun sauya ciki har da kawo karshen alakar da ke tsakaninsu da Faransa, wadda ta ke uwargijiya a wajensu.

A makon da ya wuce ne Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), ta ɗage haramcin takunkuman da ta kakaba wa Nijar.

Hakan ya sanya Shugaba Tinubu wanda shi je shugaban kungiyar bayar da umarnin sake bude iyakokin Najeriya da kasar don ci gaba da gudanar al’amuran yau da kullum ga jama’ar da yankunan iyakokin kasar.