A safiyar wannan Litinin din ce aka wayi gari da tsintuwar gawar wani mai gadi rataye a jikin lilon wata makarantar Firamare da ke Jauro a yankin Tudun Wada na Jihar Gombe.
An dai wayi gari da ganin gawar Malam Abdullahi Ardo a Firamaren mai suna Early Child Care Development Centre da har kawo yanzu ba a gano dalilin rataye kan nasa ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da faruwar da cewa sun samu labarin ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar ta Litinin.
A zantawarsa da Aminiya, ASP Mahid, ya ce Abdullahi Ardo Bafulatani ne mai shekara 38 a duniya.
“Bayan mun samu labarin jami’an mu sun je wajen sun dauki gawar zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwar sa,” inji Mahid.
A cewarsa, yanzu haka suna kan gudanar da bincike domin gano musabbabin da ya jawo ya rataye kansa.
Da wakilinmu ya tuntubi Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Gombe, Malam Babuga Audu Dolli, don jin ta bakinsa, ya ce haka kawai aka wayi gari da ganin gawar tasa ba tare da sanin dalilin rataye kansa ba.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Malam Abdullahi Ardo ya rasu ya bar Mata da ’ya’ya.