Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe.
Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista.
- An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis
- An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar wuta tare da sace kayayyakin da ta ɗauko.
“Lokacin da ‘yan sanda suka kai ɗauki, matasan sun yi musu ruwan duwatsu, sai dai an shawo kan lamarin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.”
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya bayyana jimami kan faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana damuwa kan wannan iftila’i.
A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lamarin abu ne mai girgiza zuciya.
Gwamnatin jihar ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin magani ga waɗanda suka ji raunuka, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan kare faruwar irin wannan matsala a nan gaba.