✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 10,000 a wata guda

Isra'ila ta kashe Faladinawa sama da 10,000, ta raba kimanin miliyan biyu da muhallansu cikin wata guda a Zirin Gaza

Ma’aikatar lafiyar Zirin Gaza da ke karkashin Hamas ta ce zuwa yanzu, Falasdinawan da bama-baman Isra’ila suka kashe a Zirin Gaza a wata guda sun haura 10,ooo, ciki har da kananan yara sama da 4,000.

Yakin da Isra’ila ta kaddamar ranar 7 ga Oktoba, 2023 a Zirin Gaza shi ne mafi muni a shekaru 75 da suka gabata.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin wata guda Falasdinawa sama da miliyan biyu sun rasa muhallansu a sakamakon hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza, yankin da Isra’ila ta yanke ruwan sha da wutar lantarki.

Duk da kiraye-kirayen Sakataren Majalisar ga Isra’ila na dakatar da kisan gillar, Fira Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kiran.

Netanyahu ya ce babu maganar tsagaita wuta gaba daya, har sai an sako mutanen da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta yi garkuwa da su sannan, ya ce gudanar da tsaron Gaza zai koma hannun kasarsa idan kurar ta lafa.

Ga muhimman abubuwan da suka faru a cikin wata guda da Isra’ila ta shafe tana luguden bama-bamai a Gaza:

– Harin Hamas –

A safiyar 7 ga watan Oktoba Hamas ta harba daruruwan rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra’ila, kuma mayakan kungiyar suka kutsa zuwa Kudancin Isra’ila ta sararin samaniya da kan tudu da kuma ruwa.

Isra’ila ta ce mayakan Hamas sun sace mutum 270 bayan wasu 1,400 da suka kashe a wani gangamin casu da wasu unguwanni da ke kusa da iyakar Gaza.

Fira Minista Benjamin Netanyahu ya ce rabon Yahudawa da irin harin tun lokacin da Hitler ya yi musu kisan kiyashi, don haka ya kuma lashi takobin ‘murkushe Hamas’, kungiyar da kasarsa da Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ’yar ta’adda.

– Martanin Isra’ila –

Ba da jimawa ba jiragen Isr’aila suka shiga yin luguden bama-bamai a Gaza a yayin da take ci gaba da artabu da mayakan Hamas a Kudancin kasarta.

A ranar 9 ga watan Isra’ial ta sanar da rufe Gaza gaba daya, ta yanke wutar lantarki da ruwan famfo da kuma hanyoyin jigilar abinci da sauran bukatu da ma sufuri a Gaza mai yawan al’umma miliyan 2.4.

A ranar 10 ga Oktoba Isra’ila ta mamaye Gaza.

13 ga wata, Isra’ila ta bukaci Falasdinawa su fice dagan Arewacin Gaza su koma Kudanci cikin awa 24.

Daruruwan Falasdinawa sun bi umarnin, wanda Kungiyar Kasashen Larabawa ta yi tir da shi a matsayin ‘tashin dole’.

– Yaduwar yakin –

A makwabtansu kuma, Isra’ila na musayar wuta da kawar kungiyar Hamas, wato Hezbollah da ke kasar Lebanon.

Ranar 13 ga watan aka jikkata ’yan jarida 6 daga kafofin AFP, Reuters da Al Jazeera a Kudancin Lebanon a harin da gwamnatin kasar ta zargi Isra’ila.

– Harin asibiti –

17 ga Oktoba Isra’ila ta kai harin bom a Asibitin Al-Ahli da ke Kudancin Gaza, ta kashe akalla mutum 471 a cewar hukumomin Gaza.

Isra’ila ta musanta kai harin, wanda ta zargi kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad da kuskuren kaiwa.

Dubban mutane a fadin duniya sun yi zanga-zangar Allah-wadai da harin.

– Hamas ta saki mata 4 –

Ranakun 20 da kuma 22 Hamas ta sako mata hudu daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su a Isar’ila.

28 ga Oktoba ta ce a shirye take ta sako mutanen da ke hannunta, a yi musayarsu da Falasdinawan da ke gidajen yarin Isra’ila.

30 ga Oktoba Isra’ila ta ceto wata sojarta da Hamas ta yi garkuwa da ita a yayin wani samame.

– Shigar da kayan agaji Gaza –

21 ga Oktoba, rukunin farko na manyan motoci dauke da kayan agaji suka fara shiga Gaza ta iyakar Rafah daga kasar Masar.

Zuwa ranar 3 ga Nuwanba, motoci sama da 370 suka shiga Gaza daga nan.

– Tsanantar hare-hare –

21 ga watan Oktoba Isra’ila ta tsananta kai hari a Gaza

22 ga wata, washegari, Iran ta yi gargadi cewa kazamin yaki mara misali na iya barkewa a yankin Gabas ta Tsakiya idan Isra’ila ta ci gaba da barnar da take a Gaza.

– Karya dokokin jikin MDD –

Ranr 24 ga Oktoba, Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da “yadda ake keta dokokin ayyukan jinkai na duniya” a Gaza.

MDD ta sanar cewa Falasdinawa sama da miliyan 1.4 sun rasa gidajensu tun daga lokacin da Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.

– Shigar tankokin Isra’ila Gaza –

Ranar 26 ga Oktaba tankokin yakin Isra’ila suka shiga Gaza na tsawon awanni.

Washegari Babban Zauren MDD ya yi kira da a yi “gaggawar hawa teburin sullhu” tsakanin bangarorin da ke rikicin.

Ranar 27 ga watan rundunar sojin ta sanar cewa ta fadada hare-harenta a Gaza.

Fira ministan Israi’ila Netanyahu ya sanar da mataki na biyu na yakin tare da cewa ‘tsagaita wuta ba zai yiwu ba’.

Ranar 29 ga Oktoba, Shugaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, Karim Khan ya ce hana shigar kayan jinkai Gaza na iya zama “babban laifi”.

Ranar 31, sojoji Isra’ila suka suna gwabza kazamanin yaki a cikin Gaza.

– Kaura zuwa Masar –

Ranar 1 ga watan Nuwamba kasar Masar ta bude iyakar Rafah inda Falasdinawa da aka jikkata da kuma ’yan kasashen waje suka samu ficewa daga Gaza.

Masar ta ce za ta taimaka wajen kwashe baki da masu shaidar zama ’yan wasu kasashe ‘kusan su 7,000’ daga Gaza.

– Harim bom a sansanin gudun hijira –

Daga 31 ga Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba Isra’ila ta kai hari sau uku kan sansanin ’yan gudun hijira na Jabaliya da ke Arewacin Gaza.

Ta kuma kai hari a wasu makarantu hudu da Majalisar Dinkin Duniya ta tsugunar da Falasdinawan da suka rasa gidajensu.

Kwararrun MDD kan kan kare hakkin dan Adam sun ce “lokaci na neman kurewa na dakile kisan kare dangi a Gaza.”

– Zagaye Gaza –

Bayan kusan mako guda da kaddamar da hari ta kan tudu a Arewacin Gaza, a ranar 2 ga Nuwamba Isra’ila ta sanar cewa sojojinta sun yi wa birnin Gza Gaza kawanya.

3 ga Nuwamba ta fara mayar da dubban ma’aikatan Falasdinawan da harinta ya ritsa da su.

A ziyarsa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya ce Isra’ila na da hakki da kuma ’yancin kare kanta, amma ya bukaci ta kare fararen hula Falasdinawa a Gaza.

Amma ya ce babu hanyar da Isra’ila za ta samu tsaro da ya wuci samar da kasar Falasdinu.

– Gargadin Hezbollah –

Shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah ya gargadi Isra’ila ta daina kai hari Lebanon ko ta shirya wa duka bin da ya same ta, ciki har da yaki.

Hamas ta ce harin Isra’ila ya hallaka mutane a motar daukar marasa lafiya a kusa da asibiti mafi girma a Gaza.

4 ga Nuwamba, Blinken ya sanar da goyon bayan Amurka na “kai kayan jinkai” Gaza, amma Netanyahu ya ki amincewa.

Shugaban sojin Isra’ila, Janar Herzi Halevi ya ziyarci sojojinsa a Gaza.