✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta yi wa manoma 13 yankan rago a Borno

An ruwaito cewar maharan sun yi sa manoman kisan gilla a gonakinsu.

Akalla manoma 13 ne aka yi wa yankan rago, wasu da dama suka bace a wani hari da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai gonakinsu a Karamar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.

An ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun afka wa gonakin shinkafa, inda suka damke manoman da suke aikin girbin amfanin gonakinsu a yankin Karkut da Koshebe a karamar hukumar Mafa, inda suka yi musu yankan rago.

Majiyoyin tsaro sun ce an gano gawarwaki 13 a yayin da ake ci gaba da neman mutanen da suka bace.

“Muna bakin cikin wannan lamari da ya sake afkuwa, mun rasa manomanmu fiye da 10 daga Zabarmari da aka kai wa hari da yammacin Lahadi a lokacin da suke aiki a gonakinsu na shinkafa.

“Mutanen garin gaba daya suna cikin juyayi. Hukumomin tsaro da CJTF na ci gaba da neman wadanda suka bace amma kawo yanzu an gano gawarwaki 13,” in ji wata majiya.

“An gano gawarwaki tara a daren ranar Lahadi, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka tsere daga hare-haren,” in ji majiyar.

Wata majiyar jami’an tsaro ta ce ’yan ta’addan ne a kan babura dauke da muggan makamai suka kai harin, da suka yi wa manoman yankan rago.