✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Kano: Aminiya za ta kawo labarai kai-tsaye daga kotun daukaka kara

Aminiya za ta kawo rahotanni kai-tsaye daga Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Abuja kan shari'ar zaben Gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf da…

A yau Litinin Kotun Daukaka Kara ta Tarayya za ta saurari karar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya daukaka kan soke zabensa.

Aminiya za ta kawo muku rahotanni kai-tsaye daga kotun da ke zamanta a Abuja kan shari’ar zaben tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da babban abokin hamayyarsa, Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC.

Abba ya daukaka kara ne bayan a watan Satumba kotun sauraron karar zaben gwamnan Kano ta soke nasararsa a zaben watan Maris, ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara.

NNPP da Abba, wanda shi ne kadai gwamnanta, sun bayyana hukuncin kotun farkon a matsayin rashin adalci, suka kuma daukaka kara da fatan za ta dawo masa da kujerarsa.

A ranar 20 ga watan Satumba, 2023, alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin mai shari Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay suka soke nasarar Abba, bayan sun soke 165,663 daga cikin kuri’un da ya samu a matsayin ba halastattu ba.

Alkalan sun soke kuri’un ne bisa hujjar rashin kwanan wata da kuma rashin hatimin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a jikin takardun kuri’un, abin da Gwamna Abba ya kira “rashin adalci” da kuma yi wa “tsarin shari’a dibar karan mahaukaciya.”

A ranar 18 ga watan Maris INEC ta ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da kuri’u 1,019,602 a yayin da Gawuna ya zo na biyu da kuri’u 890,705.

Amma bayan soke 165,663 daga kuri’un da Abba ya samu, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta bayyana bayyana cewa kuri’unsa sun koma 853, 939, a yayin da Gawuna mai kuri’u 890,705 ya sha gabansa.

Hakazalika kotun ta ayyana Gawuna a halastaccen zabebben Gwamnan Jihar Kano, ta umarci INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe, ta kuma soke na Abba.