Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Oyo ta lashe zaben duk ƙananan hukumomi 33 da aka gudanar a faɗin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan kammala zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli da aka gudanar a ranar Asabar.
Hukumar zaɓen jihar (OYSIEC) ta bayar da sanarwar cewa jam’iyyar PDP ce ta yi nasarar lashe zaɓen duka ƙananan hukumomi 33 a faɗin jihar.
- Ƙyanda ta yi ajalin yara 19 a Adamawa
- Naɗin sarautar Hausawa ta haddasa saɓani da fadar Oba na Benin
Shugaban hukumar zaɓen, Aare Isiaka Abiola Olagunju (SAN) ne ya bayyana sakamakon zaɓen yau Lahadi a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban ofishin hukumar da ke Agodi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Mista Abiola ya bayyana farin cikin yadda aka gudanar da zaɓen lami lafiya sabanin yadda zaɓukan baya suka riƙa fuskantar ƙalubale iri-iri.
Ya tabbatar da cewa hukumar ta samu korafe-korafe a kan matsalar rashin zuwan jami’an hukumar da kayan aiki cikin lokaci a wasu rumfunan zabe.
Sai dai ya ce hukumar ta shawo kan wannan matsala tun kafin a fara zaben na ranar Asabar.
Rahotannin da Aminiya ta tattaro sun nuna cewa jam’iyar adawa ta APC a Jihar Oyo tun kafin a kammala kada kuri’u a ranar Asabar din ta fara caccakar yadda aka gudanar da zaben.
An ruwaito cewa, APC ta nemi Hukumar Zaben ta OYSIEC ta soke zaben gaba daya tare da tsayar da ranar sake sabon zabe.
APC ta yi wannan kira ne kan dalilan matsalolin rashin isar jami’an hukumar zaben da kayan aiki kan lokaci a wasu rumfunan zabe da karancin kayan aiki da rufe wasu rumfunan da aka yi ba tare da cikakken bayani ga masu ruwa da tsaki ba.
Wani jigo na APC kuma Shugaban Kwamitin Harkokin Zabe a Majalisar Dattawa, Sanata Sharafadeen Alli, ya shaida wa ’yan jarida cewa “ku ne shaida domin ga ni yanzu da karfe 11 na safe na zo jefa kuri’a a rumfar zabe ta Unguwar Oke-Aremo a Ibadan amma babu wata alamar bayyanar jami’an hukumar zabe a wannan wuri.
“Wannan alama ce da ta bayyana a fili cewa, da gangan aka kulla wannan makirci.”
Shi ma tsohon Ministan Sadarwa Adebayo Shittu cewa ya yi bai iya jefa kuri’a a rumfar zabe a garin Saki ba saboda rashin bayyanar jami’an hukumar zaben a kan lokaci.
Shi kuwa Shugaban ’yan Arewa magoyan jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa ya bayyana cewa, “tun farko [ma’aikatan zaben]sun boye wasu akwatunan kada kuri’u kuma da mutanenmu suka ziyarci Hedikwatar Karamar Hukumar domin yin korafi sai aka fatattake su har da dukan da aka yi wa wasu daga cikin su.
“Hakan ne ya sa jam’iyyarmu ta APC mai son zama lafiya ta umarce mu da mu janye jiki domin gudun barkewar rikici.”
A nasa bangaren, Shugaban Jam’iyyar SDP a Jihar Oyo, Honarabul Michael Okunlade ya nemi Shugaban Hukumar Zabe ta OYSIEC Aare Isiaka Abiola Olagunju da ya yi murabus kan abin da ya kira ya gaza gudanar da tsaftataccen zabe a jihar.
Ya ce zaben na ranar Asabar “ya zama abun kunya a idon duniya idan aka kalli yadda aka gudanar da shi cikin son rai da yin amfani da madafun iko domin cimma buri.”
Da yake martani bayan kada kuri’arsa a rumfar zabe ta kan hanyar Iwo a Ibadan, Gwamna Seyi Makinde ya jinjina wa Hukumar Zaben Jihar a kan irin rawar da ta taka wajen gudanar da wannan zabe lafiya a fadin jihar.
Ya ce ba a taba yin zabe mai tsafta kamar wannan a jihar ba, inda kuma ya taya dukkan Shugabannin Kananan Hukumomi 33 da Kansilolin murnar da lashe wannan zabe.