Wasu fusatattun matasa sun daka wawa kan kayan abincin tallafin azumi da ɗan Shugaba Nijeriya, Seyi Tinubu zai raba a Jihar Gombe.
Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa bai kai ga zuwa jihar ta Gombe ba, amma kayan abinci da zai raba tuni sun isa jihar.
- Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas
- Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna matasan na wawason katan-katan na kayan abinci daga kan wata mota da ke tsaye a bakin titi.
An hangi matasan na jefa wa waɗanda ke ƙasa kayan abincin — inda suke karɓa su kama gabansu.
Kayan abincin sun haɗa da buhunan shinkafa da sikari da mai da taliya da kuma gishiri.
Rahotanni na nuna cewa motocin abinci biyu Seyi ya ware wa jihar ta Gombe, kuma tuni aka rabar da ɗaya, kafin matasan su dirarwa ta biyun.
A bayan nan dai ɗan gidan shugaban ƙasar na shawagi a wasu jihohin arewacin Nijeriya, inda yake haɗuwa da mazauna jihohin da kuma shugabannin siyasa wajen buɗa-baki.
A yayin waɗannan ziyarce-ziyarce ne kuma ɗan shugaban ƙasar yake ƙaddamar da rabon tallafin abinci ga mabuƙata da albarkacin watan azumi.
Sai dai wannan lamari na ci gaba da janyo cece-kuce a faɗin ƙasar, a yayin da wasu ke yabawa wasu ko kushe suke yi.
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi Allah wadai da rabon abincin da ɗan shugaban ƙasar ya yi a yankin Arewa, yana bayyana hakan a matsayin wani nau’i na rashin mutunta al’adun Arewa.
A cikin wani bidiyo da karaɗe shafukan sada zumunta, Lamido ya bayyana hakan a yayin wani taron buɗa-baki na mambobin jam’iyyar PDP da ya gudana a garin Bamaina da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
A makon jiya ne ɗan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed, ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya yi amfani da ziyararsa don tallafa wa matasan jihar.
Shamsuddeen Bala Mohammed ya ce bai kamata a mayar da matasan Bauchi kamar mabarata ba, sai dai a ba su damar dogaro da kansu ta hanyar ayyukan yi da horo na musamman.
Shamsuddeen ya bayyana cewa matasan Bauchi sun fi buƙatar ayyukan yi da jari, ba kayan abinci kawai ba.
Ya buƙaci a ba su tallafi kamar Keke NAPEP, kuɗin kafa kasuwanci, da kuma horo a fannin sadarwar zamani da cinikayyar kirifto domin inganta rayuwarsu.
Ɗan gwamnan na Bauchi ya ce yana da kyau a koya wa matasa yadda za su dogara da kansu fiye da ba su abinci da zai kare a rana ɗaya.
Babban dalilin da ya sanya da dama ke sukar yunƙurin Seyi, bai wuce saboda kallon da suke yi cewa yana ƙoƙarin farfaɗo da darajar mahaifinsa Bola Tinubu, da alamu suka nuna wani bangare na yankin ya fara yi wa bore.