An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi.
An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata.
Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya bude kofarsa da safe kamar yadda ya saba.
Daga nan ne ya sanar da dan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka balla kofar dakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama.
- Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72
- HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya?
Ya ce da shigan dan uwan mamamcin ya tsinci gawar masoyan biyu tsirara a bisa gado bayan da aka balla kofar dakin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya ce suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Aya ya ce, ”DPO na Ankpa na ya tura jami’an da suka je aka gano gawarwakin aka kai su asbiti a Ankpa inda aka tabbatar rai ya yi halinsa.”