✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas

Majiyar ta ƙara da cewa, "Matar ta cije kan mazaƙutar mutumin gaba ɗaya."

Wata mata da age zargin ta cije mazakutar saurayinta ta shiga hannun ’yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama matar mai shekara 43 ne bayan ta yi wa masoyin nata wannan aika-aika ne a lokacin da suke rikici a cikin gida a unguwar Mile 3 da ke yankin Diobu a garin Fatakwal babban birnin jihar.

Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye mai yawan jama’a lokacin da aka samu labarin lamarin.

A cewar majiyoyi, rikicin ya fara ne lokacin da masoyin matar ya nemi kwanciya da ita.

An bayar da rahoton cewa matar ta ƙi amincewa da buƙatar saurayin nata, inda ta zarge shi da yin amfani da ƙwayoyin masu ƙara kuzarin tsawaita saduwa.

Wani mazaunin garin da ya zanta da wakilin PUNCH  da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Saurayin matar ya fusata ne, saboda masoyiyar tasa ta ƙi amincewa da buƙatarsa.

“Ana cikin haka, ta yi nasarar kama mazaƙutarsa da bakinta kuma ta gantsara masa cizo.”

Rahotanni sun ce kururuwar mutumin ta ja hankalin maƙwabta, inda wasu suka yi yunƙurin riƙe matar kafin ’yan sanda su shiga tsakani.

Majiyar ta ƙara da cewa, “Matar ta cije kan mazaƙutar mutumin gaba ɗaya.”

Jami’an rundunar ’yan sanda reshen Nkpolu ƙarƙashin jagorancin jami’in ’yan sanda na yankin ne suka ceto ta, inda aka tsare su.

An garzaya da wanda aka ciza zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba a cikin birnin domin kula da lafiyarsa cikin gaggawa.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, Sufeto Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

“Eh, zan iya tabbatar da lamarin, an kama matar (wanda ake zargi) mai shekaru 43, kuma ana ci gaba da bincike,” in ji Iringe-Koko.