✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano 

Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta.

Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta

Fitattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Rabin hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan.

Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare.

Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin danganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi.

Sanarwar ta bayyana cewa, wanda aka kama din wani makaniken babur ne wanda korafe-korafen jama’a suka yi yaw a kansa.

Ya ce, a yayin da yake tsare, ya nuna alamun rashin lafiya inda aka kai shi babban asibitin Rano, inda ya mutu da safiyar ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 6:00 na safe.

A sakamakon gaka, wasu gungun fusatattun mutane suka dkai hari a hedikwatar ’yan sanda ta Rano, inda suka cinna wuta a wasu sassan ofishin, suka lalata motoci goma, sannan suka kona wasu biyu.