Rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa a ƙauyukan Faruruwa da Tarandai da ke Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano, inda aka kashe wani matashin har lahira.
Rikicin ya faru ne a ranar cin kasuwa kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka ƙone rumfunan kasuwar.
- Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir.Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole
Wani masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar 23 ga watan Mayu, 2025, a kasuwar Faruruwa.
A cewarsa, rikicin ya samo asali ne bayan wani matashi mai shekaru 28, Sani Yunusa daga ƙauyen Toho Diribo ya ziyarci budurwarsa a Tarandai.
Yayin da yake komawa gida, wasu matasa suka kai masa hari da sanda da adda.
Jami’an tsaro sun isa wajen cikin gaggawa don daƙile rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta fara bincike don gano musabbabin rikicin da kuma kama waɗanda suke da hannu a kisan matashin.