✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe

Gidauniyar ta kuma tallafa wa mata guda 75 da jari na ₦15,000 kowannensu.

A ƙoƙarinta na tallafa wa marayu da mabuƙata, gidauniyar Zakkah da Wakafi a Gombe ta raba wa yara marayu da mabuƙata 100 kayan Sallah.

Da yake jawabi a lokacin rabon tufafin, Shugaban gidauniyar, Amir Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce al’adar gidauniyar ce ta riƙa zaƙulo mabuƙata tare da tallafa musu musamman a lokutan bukukuwan Sallah.

Ya bayyana cewa, a da can gidauniyar na karɓo tsoffin tufafi daga hannun masu hannu da shuni, tana tsaftacewa tare da sake ƙunshe su kafin rabawa.

Amma wannan shekarar, gidauniyar ta ɗauki sabon tsari na sayan sababbin tufafi daga matan da ta koyar da sana’o’in hannu.

Waɗannan mata da suka samu horo a sana’o’i irinsu ɗinki, haɗa sarƙa da abun wuya na mata, da kuma ƙera takalma sun samu damar sayar wa gidauniyar kayayyakin da suka ƙera.

Lamido ya ce wannan hanya ba wai kawai ta amfani da tufafi don marayu da mabuƙata ba, har ma ta ba wa mata damar ƙarfafa musu gwiwa  kan kasuwanci.

Lamido ya yi kira ga masu hannu da shuni su karkatar da zakkar su zuwa ga Zakkah da Wakafi tare da tabbatar musu cewa gudunmawarsu za ta isa ga waɗanda suka cancanta.

Ya ƙara da cewa, da dama daga cikin masu ba da gudummawa sun nuna gamsuwa da yadda gidauniyar ke gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da tasiri.

Bayan rabon tufafin Sallah, gidauniyar ta kuma tallafa wa mata guda 75 da jari na ₦15,000 kowannensu.

Waɗannan mata sun samu horo kan yadda za su sarrafa kuɗin su da kyau, ciki har da tanadin kaso ɗaya bisa uku na ribar su a cikin asusu na musamman na tsawon shekara guda don ƙarfafa kasuwancin su ya dore.

Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI), Saleh Danburan, ya yaba wa gidauniyar bisa ƙoƙarinta na taimakon al’umma tare da kira da ta ci gaba da tsayawa kan turbar addinin Musulunci.

Fitaccen malamin addini musulunci Malam Bello Doma, ya jinjina wa ayyukan gidauniyar tare da bayar da shawarar kafa wani bankin al’umma don bayar da rance marar riba cikin sharuɗa masu sauƙi.

A cewarsa, wannan zai samar da taimakon kuɗi ga al’umma ba tare da kunyata su ko ƙin karɓar buƙatunsu ba yayin da suka nemi taimako.