Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam (JNI), ta raba kayayyaki da sauran kyatuttukan Sallah ga marayu 50 gabanin bikin Sallah ƙarama a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
An gudanar da bikin ba da tallafin ne a harabar makarantar sakandare ta Bulabulin da ke birnin na Maiduguri.
- Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya
- Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna
Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan kungiyar JNI reshen Maiduguri, Malam Ibrahim M. Bello, ya jaddada muhimmancin tallafa wa mabuƙata, yana mai jaddada cewa wannan shi ne babban burin ƙungiyar.
Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin da su yi amfani da kyaututtukan domin biyan buƙatunsu.
A nasa jawabin, mataimakin sakataren ƙungiyar, Abubakar Abdullahi, ya ce sun yi hakan ne da nufin sanya farin ciki da jin dadi ga yara marasa galihu a lokacin bukukuwan Sallah.
Ƙungiyar ta JNI ta himmatu matuƙa wajen taimaka wa mabuƙata, musamman marayu da ba su da abin dogaro da kai in ji Abubakar.
Ya kara bayyana cewa, an zabo waɗanda suka samu tallafin ne bisa sharuɗan da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta gindaya.
A cewarsa, ƙungiyar ta shafe sama da shekaru goma tana gudanar da irin waɗannan ayyuka na agaji.
Abdullahi ya kuma yi kira ga iyaye, hukumomin gwamnati, da shugabannin masana’antu da su haɗa hannu wajen ganin an samu sauƙaƙa rayuwar marayu.
Ya yi nuni da cewa, wannan ƙoƙari na haɗin gwiwa zai taimaka matuƙa wajen tallafa wa yara masu rauni da kuma inganta fahimtar al’umma dangane da zamantakewa.