✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hanzarta kwangilar yashe Madatsar Ruwa ta Alau — Gwamnatin Borno

Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala.

Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alau da ya haifar da ambaliya a bara.

Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam ɗin amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mummunar ambaliya.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na Jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin.

“Har yanzu ba mu ga ’yan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka.

“Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala.

“Ya kamata a ce an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba zai ambaliya ba,” in ji Farfesa Tar.

A damunar bara ne dai madatsar ruwa ta Alou Dam ta cika ta tunbatsa inda ta kuma karye, wani abu da ya janyo ambaliyar ruwa da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Maiduguri.