Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa.
- Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
- Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
ICRC ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 3.7, wadanda galibi manoma ne na fuskantar barazanar matsanancin rashin abinci a yankin da aka shafe shekaru ana rikici.
Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma, ya ce farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, kuma kudin ɗinki da yake samu da dare bai isansu.
Modu Umar, wani shugaban al’umma, ya bayyana cewa yunwa tana haddasa cututtuka kamar gudawa a cikin yara da manya saboda rashin abinci da magani.
“Mutane na fita nesa su tara itace domin samun kudin siyan abinci,” in ji shi.
ICRC dai ta ce ta fara wani shiri na taimaka wa noma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga sama da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.
“Ana kuma shirin rarraba famfunan ban-ruwa masu aiki da hasken rana domin noman rani,” in ji ƙungiyar ICRC.
Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta ce ana fargabar za a fuskanci matsanancin ƙarancin abinci daga Yuli zuwa Satumba, inda mutane ke buƙatar sayen abinci, amma ƙarancin kudi yana hana su cika buƙata.
A cewarta, matsananciyar yunwar na janyo tsamurewar jiki saboda rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin ƙananan yara ’yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu shayarwa.
Ƙungiyar ICRC na aiki a Borno tun 2012 inda take taimaka wa al’ummomin da rikici ya shafa da kuma kare martabar fararen hula bisa dokokin Geneva na 1949.