Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.
A cewar kungiyar, jihohin su ne Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano.
Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar, Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudana a Kano ranar Talata.
- Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista
- Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja
Ya ce daga cikin adadin, akalla yara miliyan daya da dubu 900 ne kuma ke fama da matsanancin karancin abincin, yana mai bayanin cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rashin tsaro da karancin abinci.
Dr Aminu ya ce, “Mun fahimci cewa ana samun yaduwar cutar yunwa da sauran cututtuka kamar su maleriya da amai da gudawa da kuma kalubalen tsaro a wasu sassa na Najeriya, don haka ya zama wajibi a dauki matakan kariya da kuma wayar da kan jama’a ta hanyar hada kai da mutane domin lalubo bakin zaren.
“Duk inda ake da matsalar tsaro, mutane kan kyale gonakinsu su bar yankunan. Sannan mutane da dama sun rabu da muhallansu sun koma ’yan gudun hijira a wasu wuraren. To duk lokacin da aka raba ka da hanyar samun abinci, akwai barazanar fuskantar matsalar yunwa.
“Sannan ba wai iya maganar abinci kawai ake ba, magana ce ta abinci mai gina jiki da kuma ruwan sha mai tsafta,” in ji shi.
Shi ma shugaban kungiyar a Najeriya, Prince Oluyemisi Adetayo Adeaga, ya ce karancin abinci babbar cuta ce da ke bukatar agajin gaggawa saboda kada ta ta’azzara.
“Idan ka je asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu, za ka ga yadda jama’a ke tururuwar zuwa saboda cututtukan da ke da alaka da yunwa. Hakan na da barazana ga dan Adam da ci gaban kasa,” in ji shugaban.
Shi ma shugaban kungiyar a Kano, Barista Salisu Sallama, ya ce kodayake jihar ba ta da yawan masu fama da cutar idan aka kwatanta da takwarorinta, amma akwai barazana idan aka yi la’akari da halin da ake ciki da zai iya ta’azzara matsalar a nan gaba.