✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abincin karnuka ya fi wanda ake ba mu —Fursunonin Najeriya

Yawancin ursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.

Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi.

Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.

Wani fursuna a gidan yarin Goron Dutse a Jihar Kano ya shaida wa wakilinmu cewa ɗanyen abinci ake ba su, yayin da wasu a gidan yarin Ikoyi a Jihar Legas suka ƙara da cewa ko kare ba zai iya cin abincinsu ba, saboda waken kamar daga kwata aka ɗebo, ga tarin tsakuwa da ƙwari da kuma datti a ciki, miyar kuma kallonta kawai zai iya sa mutum hararwa.

Gidan Yarin Goron Dutse

Wani tsohon fursuna a Gidan Yarin Goron Dutse wanda aya kammalawa wa’adi sa na wata 18, ya bayyana cewa, ɗanyen abinci ake ba su.

Ya ce, “daga baya aka bari muka fara yin girki saboda abincin ba ya wadatarwa. Fursunonin da suke jin daɗi su ne masu zaman ɗaurin rai-da-rai da kuma waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.”

Majiyoyi a gidan yarin sun bayyana mana cewa abinci ninki biyu ake ba wa fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa, kuma musamman ake dafa musu abincinsu, musamman kunu, tuwo, wake ko shinkafa.

Ci-kar-ka mutu

A gidajen yarin Jihar Borno Aminiya ta samu labarin cewa abincin da ake ba fursunoni bai taka kara ya karya ba.

Wata majiya ta ce, “Gwamnati ta mayar da su kamar dabbobi ba mutane ba, kullum dan kwangilar da aka ba aikin ciyarwan ƙorafin tsadar kayan abinci yake yi, don haka ba zai iya samar da isasshen abincin da zai wadai fursunonin ba.

“Abin da suke yi yanzu shi ne rage yawan lokutan da ake ba da abincin a wata. Misali dan a mako suna ba da shinkafa sau hudu a mako, to wani wata sai su rage su maye gurbinta da abinci mara tsada kamar garin rogo, wani lokaci kuma yi tsallake.”

Ya ƙara da cewa tsadar icen da ake girki shi ma ya kara dagula lamarin, “Amma muna fata idan Gwamnatin Tarayya ta Kara kudin ciyarwan a kara abincin.”

Kamar a gidan soja

Tony, wani fursuna a Gidan Yarin Ikoyi a Jihar Legas, wanda ya bayyana cewa an mayar da tsarin ba su abinci kamar aikin soja ya ce, ko kare ba zai ci abincin da ake ba su ba.

Ya ce, “yadda ka san aikin soja haka tsarin abincin yake. Sau uku ake ba mu abinci a rana, amma ko kare ba zai ci ba. Taimakonmu ɗaya, shi ne aka bari wasunmu su sayi abinci a shagon da ma’aikata ke sayen kayayyaki. Ina tabbatar maka, duk wanda ya ce zai dogara da abincin da hukumar ke bayarwa, ya ba zai rayu ba.

“Yawancin fursunonin ana kai su asibiti saboda tamowa. Kullum da safe wake ake ba mu, da rana kuma teba da wata miya ruwa ruwa, babu kifi ko nama, da dare a ba mu busasshen garin rogo.

“Haka ake ba mu waken cike da tsakuwa da kwari da datti, saboda ba a tsince ta da kyau, sannan za ka iya kirga ƙwayoyin waken da ake ba wa mutum.

“Cokali ɗaya ko biyu na wake cike da ruwa za ake ba wa kowa sai busasshen garin rogo. Ni a ciki nake zuba garina domin ya tsira ruwan.”

Tony wanda ya ce ko kaji sai dai su yi malejin abincin ya kara da cewa, “ba na cin abinci duk lokacin da aka yi teba da miyar kuɓewa ko gushi. Farkon zuwana da na ci zai da na yi amai, amma daga baya dole ya sa na dawo ina ci. Kallon miyar kaɗai ma zai iya da mutum hararwa,” in ji Tony.

Ya ci gaba da cewa, “za ka iya ware ruwan miyar gefe, agsuhin ma gefe, waken kuma yadda ka san daga kwara aka ɗebo, haka yake.”

Shi ma wani fursuna da ke tabbatar da iƙirarin Tony a Gidan Yarin Ikoyi, ya bayyana cewa, “abincin babu kyau, yawanci idan da ci waken, wanda ba ya nuna sosai, yini nake ina yin zawo, wani lokaci nakan gwammace in zauna da yunwa a kan in ci.”

Wani jami’in gidan yarin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa, “sau biyu ake ciyar da fursunonin saɓanin sau uku da aka tsara a hukumance.”

Ganin kifi sai ɗan baiwa

Wani fursuna a gidan yarin da wakilinmu ya zanta da shi a Kotu da ke yankin Igbesore a Jihar Legas, ya ce ba fursunonin ke yin girki ba, inda ya bayyana cewa ma’aikatan gidan yarin ko wadanda aka ba wa kwangila ne suke yin girki.

“Abin mamakin shi ne sai ka rasa wa ina kifin da nama suke zuwa. Fursunonin da suka mayar da kawunansu hukuma a cikin sel-sel ne ma ke da alfarmar cin kan kifi. idan har ka yi sa’ar ganin burbushin kifi a abincin to ka zama ɗan baiwa, ko da yake waɗanda rabonsu ya tsaga suna aiki a ɗakin girki suna samu su ci ƙarin abinci bayan wanda ake bayarwa na ƙa’ida.”

Shi ma ya tabbatar cewa sau biyu ake ba su abinci, da safe da kuma dare, wanda bai wuce wake da shinkafa da teba da wata miya ruwa-ruwa, wadda za a iya ware ruwan miyar daban, agsuhin kuma gefe ɗaya.

Wannan zarge-zargen na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari.

A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida,  Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin.

Duk da cewa kwamitin ya tabbatar da zargin yunwa da fursunonin suka yi, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Kasa, ya ce an zuzuta lamarin, saboda a cewarsa, babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.