✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina

Gidauniyar ta ce za ta ci gaba da irin wannan aikin don rage cunkoso a gidajen yari.

Gidauniyar Daily Trust (DTF) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar WRAPA, Hamu Legal, da Bahama Chambers, sun biya tarar fursunoni 21 domin su samu damar fita daga gidajen gyaran hali a Jihohin Kaduna da Katsina.

A Kaduna, an ’yanta mutum 17 bayan da DTF da abokan aikinta suka biya tarar su har Naira miliyan biyu da dubu dari biyu.

Laifuffukan da aka yanke musu hukunci sun haɗa da sata, shiga da karɓar kayan sata.

Da yake jawabi ga waɗanda aka fitar, Daraktan Gidauniyar Daily Trust, Dokta Theophilus Abbah, ya ce manufar shirin shi ne rage cunkoson fursunoni da kuma bai wa waɗanda suka aikata ƙananan laifuka damar gyara rayuwarsu.

Ya kuma yi kira a gare su da su koma cikin al’umma su rayu cikin gaskiya da riƙon amana.

Jami’in shirin WRAPA, Paul Adama, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da bayar da tallafi a ɓangaren shari’a domin ganin irin wannan aiki ya ci gaba da gudana.

A Jihar Katsina kuwa, an ‘yanta fursunoni huɗu cikin haɗin gwiwa tsakanin WRAPA da DTF.

Ɗaya daga cikinsu wani matashi ne daga Batsari wanda ya rasa iyayensa a harin ’yan bindiga kuma aka kama shi da laifin satar Naira 60,000.

Ya ka sa biyan tarar Naira 10,000 da diyyar Naira 60,000 har sai da Gidauniyar Daily Trust ta biya masa.

Mataimakin Konturola na Katsina, Lawal Talle, ya jinjina wa Gidauniyar Daily Trust da abokan haɗin gwiwarta bisa wannan taimako.

Sai dai kuma ya gargaɗi waɗanda aka ’yanta da su guji komawa aikata laifuka.