✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu

Maniyyata 4,060 daga Jihar Kaduna ne za su sauke farali a bana

Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025.

Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin Hajjin bana.

Ya bayyana cewa maniyyata 4,060 daga jihar Kaduna za su sauke farali a bana, kuma kamfanin jirgin sama na UMZA ne zai yi jigilarsu.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa domin kammala matakan da ake bi kafin tafiya, za a yi duk maniyya cikakken gwajin lafiya a sansanin alhazai da ke Mando.

Ka’idodin lafiya na ƙasa da ƙasa da kuma na Saudiyya sun shardan cewa dukkan mata maniyyata za su yi gwajin daukar ciki kafin tafiya.

Malam Salihu ya bukaci maniyyata su kiyaye dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Saudiyya suka gindaya, yana mai jaddada muhimmancin ladabi, haɗin kai da kuma kiyaye tsaron kai a lokacin aikin Hajji.

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da sadaukar da kai don ganin maniyyata sun sami sauƙin tafiya tare da samun damar ibada cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.