Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin.
- Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum
- Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
Mista Fanwo ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna biyu daga cikin waɗanda suke tsere ɗin.
Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin.
Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne.
“Dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu,” in ji Fanwo.
A yayin da gwamnatin ke yaba wa jami’an tsaro dangane da matakin gaggawa da suka ɗauka kan lamarin, ta kuma buƙaci mazauna da su zama masu lura da bai wa mahukuntan haɗin kai.
“Muna kiran al’umma da su miƙa rahoton duk wani da motsi da ba su aminta da shi ba, sannan duk wanda aka kama yana bai wa fursunonin mafaka ko taimaka musu zai ɗanɗana kuɗarsa.”