2024 shekara ce da ta ke cike da rikici, sabani, zanga-zanga da tashe-tashen hankula a Najeriya, lamarin da ya sanya aka samu zubar da jini da yanayin dari-dari.
A wannan shekara ta 2024 da muke bankwana da ita, an fuskanci manyan shario’o’i da suka yamutsa hazo a Najeriya. Waɗannan kuwa sun haɗa da shari’ar yara masu zanga-zangar yunwa da ta rikicin masarautun Kano da shari’ar Emefiele da ta tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da sauransu.
Wannan ne ya sa Aminiya ta yi waiwaye tare da ɗauraya, domin sake kawo wa mai karatu irin wainar da aka toya a shekarar da muke bankwana da ita.
Shari’ar masarautun Kano
Idan akwai wani abin da za a manta ya faru a shekara 2024, to tabbas banda dambarwar Masarautun Kano, domin kuwa, al’amari ne da ya dauki hankali mutane a ciki da wajen Najeriya, kuma har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana ba tsakanin gwamnati da bangarorin da ke ikirarin halascin sarautar kowannensu.
- Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9
- ’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos
- Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda
A watan Yuni ne Gwamnat Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar dokar masarautu, wadda ta rushe sabbin masauratu biyar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro, ta kuma bai wa Gwamnan damar dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki na 16.
Bayan sanya hannun a kan dokar sabbin masarautun suka dauki dangana, banda Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda a lokacin yake kasar waje, amma ya dawo Kanoya tare a karamar fadar Nassarawa.
A yayin da lamarin ke kotu, bangaren Sarki Aminu sun shigar da karar neman soke nadin Sarki, a yayin da gwamantin ke neman tabbatar da shi da samun umarnin hana Aminu bayyana kansa a matsayin basaraken Kano.
Lamarin dai ya haifar da rudani, inda gwamnatin jihar ke zargin ya samu goyon baya daga gwamnatin tarayya da ke neman mayar da shi kan kujera da karfin tsiya, inda aka jibge masa jami’an tsaro da ke gadin fadar Nassarawa.
Dambaruwar masarautar Kano ta kai ga kowane tsagi ya shigar da kara s kotu, wanda hakan ya sa kotu yanke hukunci mabambanta. Har yanzu haka dai ana ci gaba da wannan shari’ar.
Lamarin dai ya kai yin musayar kalamai tsakanin tsagin gwamnatin APC da NNPP s Kano. Sai dai masu ruwa da tsaki da shugabanni sun yi kira da yi sulhu domin samun zaman lafiya a jihar.
Shari’ar ’yan zanga-zangar yunwa
A shekarar ce kura ta tashi na Najeriya da kasashen waje bayan gwamantin Najeriya ta gurfanar da kananan yara a kotu kan zargin yunkurin kifar da gwamnati a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa da aka yi a kasar a wata Agusta.
A lokacin gurfanar da yaran wadanda aka tsare na tsawon watanni a gidan yarin Kuje ne wasu daga cikinsu suka sume, babu shiri Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da zaman, kafin daga bisani Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya ci gaba da zaman bayan an fitar da su domin duba lafiyarsu.
Daga baya alƙalin ya bayar da su beli a kan Naira miliyan 10 kowannensu tare da umarnin tsare su a Gidajen Yarin Kuje har sai an cika sharuɗan belin da suka hada da kawo wani babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ya tsaya musu. Haka kuma za su kawo takardar kyakkyawar shaida daga iyayensu ko kamu ’yan uwansu.
Wannan hukunci ya bar baya da kura, inda dubban mutane suka fara sukar gwamnatin Najeriya, inda a karshe Shugaba Tinubu bayar da umarnin sakin su, gwamnatin tarayya ta mika yaran ga gwamnnonin jihohinsu.
Shari’ar zaben Gwamnan Kano
A ranar 12 ga watan Janairu 2023 ne, Kotun Koli ta tabbatar wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP kujerarsa inda ta soke hukunce-hukuncen da kotunan baya masu cike da rudani da kuma karo da juna.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun Dauka Kara ta Tarayya ta yanke, inda ta kwace kujerar Abba, amma takardar hukuncin da ta fitar kuma ta tabbatar masa da kujerar.
Kotun Koli ta sanar da hukuncin ne bayan ta yi watsi da kararrakin da APC ta shigar na zargin aringizon kuri’u da kuma ikirarin cewa Abba ba halastaccen dan NNPP ba ne, da ke da hurumin shiga zabe.
Alkalin da ya karanta hukuncin, Mai Shari’a Inayng Okoro, ya sanar cewa kotun daukaka kara ta yi kuskure wajen soke kuri’un Abba da ake takaddama a kan sahihancinsu, hasali ma, babu hujjar da ta tabbatar cewa ba su ne aka jefa a zaben ba. Sannan batun zaman Abba dan takarar gwamna a NNPP abu ne na cikin gidan jam’iyyar, don haka wanda ba dan jam’iyyar ba shi da hurumin tsoma baki a ciki.
Mai Shari’a Okoro ya shawarci alkalai da su rika yin duba na tsanaki kan kararrakin da aka kawo gabansu kafin su yanke hukunci.
Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano tana kalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna ba Abba ba. Bayan nasarar APC a shari’ar farko ne Abba da NNPP suka garzaya zuwa Kotun Ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya.
Sau biyu gwamnan Kanon yana daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya da suka kwace kujerarsa.
Shari’ar Kwamishinan Jigawa da matar aure
A 20234 ne Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ayyana Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Sankara a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo sakamakon zargin sa da yin lalata da matar aurr, bayan karar da mijin matar Nasiru Buba, ya kai mata.
Sai dai daga bisani bayan zuwa kotu da sauran su, kotun Muslunci da ke Kano ta wanke Kwamishinan wanda gwamnatin Jigawa ta dakatar shi saboda lamarin, daga zargin aikata zina d matar aure.
Tsohon mijin matar, Nasiru Buba ne, ya kai ƙarar, inda ya zargi Sankara da mu’amala da matarsa, Tasleem Baba Nabegu. Alƙalin ya bayyana cewa binciken da ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya gudanar, ya nuna cewa babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da ake yi wa Sankara.
Kotun ta kuma lura cewa Nasiru Buba da lauyoyinsa ba su halarci zaman kotun ba don ƙalubalantar sakamakon binciken ’yan sanda. “Tunda wanda ya shigar da ƙara da lauyoyinsa ba su zo ba don su ƙalubalantar rahoton, ba ni da zaɓi face na yi watsi da ƙarar,” in ji alƙali Sarki Yola.
Shari’ar Badaƙalar iyalan Ganduje
Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da iyalansa sun fuskanci shari’a bisa zargin da gwamntin jihar ke musu da wasu makusantansa da cin hanci da karkatar da dukiyar al’umma. ِ
Ganduje bai taba halartar zaman Babbar Kotun Jihar Kano da ke sauraron ba, wanda Hukumar yaki da almundahana ta jihar ke zargin sakarkatar da kudaden kananan hukumomi Naira biliyan 51.3 da fitar da Naira miliyan 600 daga asusun gwamnatin jihar zuwa wani kamfani da yake matsayin darakta kuma mai dakinsa ke gudanar da asusunsa.
Wasu dai na zargin binciken da hukumar ke wa Ganduje da iyalinsa ramuwar gayya ce kan dakatarwar da ya yi wa shugaban hukumar, Muhyi Rimingado a lokacin mulkinsa. Amma Muhyi ya musanta zargin da cewa tun Ganduje na mulki hukumar ta fara binciken, wanda shi ne ma dalilin da ya sa aka dakatar da shi.
A cewar Muhuyi a zamnin mulkin Ganduje dai ya sha musanta zargin, har ya kafa kwamitin binciken wani bidiyon da ke zargin yana karbar Dala yana cusawa a aljihu, domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Shari’ar Emefiele
A 2024 EFCC ta ci gaba da gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, inda a karon farko Babbar Kotun Tarayya ta ba shi fita daga yankin Abuja bayan bukatar hakan da lauyansa, Mathew Bukka, SAN ya gabatar, yana neman ta sauya sharuddan belinsa da ta bayar.
A ranar 23 ga Nuwamba, 2023, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ba da belin Emefiele, wanda Hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ta gurfanar kan zargin badakalar biliyoyin kudade a lokacin shugabancinsa a CBN.
A lokacin, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya shardanta wa Emefiele ajiye kudi Naira miliyan 300 da kuma kawo mutum biyu wadanda kowannensu ya mallaki gida a unguwar Maitama a Abuja su tsaya masa.
Haka kuma alkalin ya shardanta wa tsohon gwamnan na CBN cewa ba zai fita daga Abuja zuwa wani waje ba. Amma a zaman na karshe, lauyansa, Matthew Bukkak, ya bakaci a janye sharadrin hana shi fita daga Abuja, yana mai cewa a matsayin Emefiele na babban mutum, ba zai tsere ba idan aka yi masa sassaucin fita daga Abuja, hasali ma takardunsa na tafiye-tafiye suna hannun kotu.
Har yanzu dai Emefiele na hannun hukumomi a tsare, inda ake ci gaba da shari’arsa.
Shari’ar Yahaya Bello
Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, bayan shafe watanni yana wasan buya da hukumar da ke zargin sa da karkatar da dukiyar jama’a kimanin Naira biliyan 1100a lokacin da yake gwamna. A karshe ya miƙa kansa ga hukumar ta kai shi kotu, inda ta tsare shi a Gidan Yarin Kuje.
Mai shari’a Maryanne Aninih, ta umarci EFCC ta tsare Bello a hannunta, tare da sanya ranar 10 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.
Lauyoyi daga ɓangarorin EFCC da Bello sun yi muhawara kan buƙatar bayar da belinsa. Lauyan Bello, Joseph Daudu (SAN), ya roƙi kotun ta bayar da belinsa, inda ya ce laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan na cikin waɗanda za a bayar da beli.
Sai dai lauya mai gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya ƙalubalanci buƙatar belin. Bello, tare da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Kogi, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, an zarge su da haɗa kai wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati don sayen kadarori a Abuja da Dubai, na kimanin Naira biliyan 110.4.
Kafin fara zaman kotun, an tsaurara tsaro a wajen kotun, inda jami’an sojoji, DSS, EFCC, da ‘yan sanda suka yi dafifi. Bello ya shiga ɗakin kotun sanye da farar babbar riga da hula mai launin shuɗi mai haske.
Sai dai hakarsa ta cimma ruwa a ranar Juma’a 20 ga watan Disamaban 2024, inda kotun ta bayar da belinsa kan wasu sharuda.
Shari’ar Murja da Hisbah
Fitacciyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya da Hukumar Hisbah ta jihar Kano sun kai ruwa rana kan batun bata tarbiyya, inda Hukumar ta gurfanar da Murja kan zargin Murja da yada kalaman batsa da koyar da karuwanci a kafafen sada zumunta.
Bayan kotu ta ba da umarnin tsare Murja a gidan yari ne ‘yar TikTok din ta yi layar zana daga gidan yarin, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce, kafin daga bisani jami’an gwamnatin jihar su amsa cewa an dauke ta ne domin ba ta kariya.
A baya kotun Musulunci ta yanke mata hukunci da wasu na yin sharar Asibitin Murtala da ke Jihar. Har ila yau, Hisbah ta sake gurfanar da Murja a kotun Musulunci da ke unguwar Hausawa, inda kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin watanni uku a gidan gyaran hali.
Daga bisani Murja, ta yi karar hukumar Hisbah, a babbar kotun jihar inda ta bukaci Hukumar ta zo ta yi mata bayani kan wasu dokokinta masu cin karo da juna.
Lauyoyin Murja Ibrahim Kunya sun kalubalanci dokar Hisbah da cewa ta saba wa Kudin Tsarin Mulkin Najeriya. Dokar da ake takkadama a kai ita ce Hisbah ke amfani da ita wajen kama masu laifi.
Kotun ta kuma umarci akawun Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bayyana a gabanta domin yin cikakken bayanin dalilin da majalisar ta samar da dokokin masu kama da juna a rana daya.
Duba da rashin gamsuwar kotu game da Sashe na 10 na dokar Hukumar Hisbah Alkalin Kotun Mai sharia Nasiru Saminu ya bayar da wadancan umarni inda kuma ya dage sauraren shari’ar.
Daga baya dai rahotanni sun nuna cewar Murja ta bar Kano da zama inda ta koma Jihar Legas da zama don yin rayuwa.