An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji.
DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu.
- Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo
- An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da mai sanyaya zuciya bayan damuwa da bala’in da mazauna Gaza suka tsinci kansu a ciki, yana mai fatar gaggauta shigar da kayayyakin agajin da kuma dorewarsa.
A yayin taron tattaunawa kan matsalolin da suke shafar ayyukan samar da abinci a Afrika ne Guterres ya faɗi cewa yunwa ba za ta taɓa zama makamin da za a yi amfani da ita wajen yaƙi a duniya ba.
Babban jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya yi maraba da matakin, yana mai cewa yanzu haka yana tuntubar kungiyoyi wadanda za su yi duk mai yiwuwa don isa ga mutane da dama da ke fama da yunwa a wannan lokaci.
Tuni dai kungiyoyin agaji suka gabatar da wasu korafe-korafe tun ba a yi nisa ba, don yi wa tufkar hanci muddin ana son kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukan agajin da aka fara bayan fiye da watanni uku da dakatar da su.
Ahmad Nadir, na kungiyar lafiya ta duniya WHO, ya ce tsame hannun Isra’ila daga batun karba da rabon kayan agaji ne kadai zai bai wa kwarraru kan ayyukan agaji damar gudanar da ayyukan da za a samu nasara.
A bayan nan ne Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce kashi uku na al’ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriyar tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga mutuwar wasu.
Isra’ila dai na ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya, kan amfani da yunwa a matsayin makamin yaki kan al’ummar Falasdinu, lamarin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da shi.
Akwai yunwa ta gaske a Gaza —Trump
Ko a wannan ɗin Litinin Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “akwai yunwa ta gaske” a Gaza.
Shugaban na Amurka ya faɗi hakan ne bayan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nace kan cewa babu yunwa a yankin.
Da aka tambaye shi ko ya yarda da abin da Netanyahu ya fada cewar “ƙarya ce tsagwaronta” idan aka ce Isra’ila na ta’azzara yunwa a Gaza, shugaban na Amurka ya ce: “Ban sani ba…amma yaran nan da ka gan su, suna cikin yunwa…wannan yunwa ce ta gaske.”
Kalaman Trump na zuwa ne bayan shugaban hukumar kai agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana buƙatar abinci mai “ɗimbin yawa” domin magance halin yunwa da yankin ke ciki.