Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutum miliyan 1.3 a Arewa maso Gabashin Nijeriya saboda ƙarancin kuɗi.
Darektan WFP a Nijeriya, David Stevenson, ya ce kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe.
- Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi
- 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed
Ya ce tallafin zai tsaya ne daga ƙarshen watan Yuli, lokacin da aka ƙiyasta kayan abinci da na kiwon lafiyar za su ƙare gaba ɗaya.
Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba, mutane da dama za su fuskanci yunwa, gudun hijira ko kuma shiga hannun ‘yan tayar da ƙayar baya.
A cewar Mista Stevenson, kusan mutum miliyan 31 ke fama da matsananciyar yunwa a ƙasar wanda shi ne mafi muni a tarihi.
“Yara ƙanana za su fi shan wahala, domin fiye da asibitoci 150 a Borno da Yobe da ke kula da yara ’yan ƙasa da shekaru biyu za su rufe,” in ji daraktan.
WFP na buƙatar dala miliyan 130 domin cigaba da ayyukanta har zuwa ƙarshen shekarar 2025.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa, kuma yunwa na kai matsayi mafi muni a tarihin ƙasar