✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF

An samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki.

Wani rahoto daga ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa wato Medecins Sans Frontiere na nuni da cewa sama da yara 650 ne suka mutu bayan fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki a Jihar Katsina.

Medicins Sans Frontiere wadda ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki da aka isar da su zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da ƙungiyar ke da su a yankin.

A cewarta, a tsakanin Janairu da Yuni 2025 ta yi jinyar kusan yara 70,000 da ke fama da tamowa a Jihar Katsina, ciki har da kusan 10,000 da ke bukatar kulawa da ta dace daga likitoci .

“A wannan shekarar ta 2025 a cewar ƙungiyar, yara 652 suka mutu saboda rashin samun kulawa akan lokaci,” in ji Ahmed Aldikhari, mai magana da suna ƙungiyar ta MSF a Nijeriya, kamar yada sanarwa ta tabbatar a ranar Juma’a.

MSF ta ce yaran da iyaye sun fuskanci tarin matsaloli ne sakamakon raguwar tallafin da ake samu daga ƙasashen duniya, inda manyan ƙasashe masu bayar da tallafi da suka hada da Amurka da Birtania da kuma Tarayyar Turai suka rage kudaden da suke bayarwa.

Ana iya tuna cewa a wannan makon nan da muke bankwana da shi ne Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (WFP) ta sanar da dakatar da tallafin abinci na gaggawa ga mutane milyan 1.3 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya daga karshen watan Yuli, sakamakon karancin kudade.

Ƙungiyar ta ce adadin yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki wanda ya fi kamari kuma mai barazana ga rayuwa a Jihar Katsina ya karu da fiye da kashi 200 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.