Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga bayan kimanin shekara 11 ana nemansa ruwa a jallo.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta bayyana cewa sun kama ɗan bindigar mai suna Mati Bagio wanda ke zaune a Unguwar Galadima ta Gundumar Shika a Karamar Hukumar Giwa.
- An zartar wa mutum 3 hukuncin kisa saboda laifin fyaɗe a Iran
- Abin da ya hana Ganduje zuwa tarbar Tinubu a Kano
Kakakin rundunar, Mansir Hassan ya ce Bagio mai kimanin shekara 34 ya daɗe yana addabar yankunan Giwa da Hunkuyi a Kaduna, da Faskari da Dandume da Funtua a Jihar Katsina.
“Mun kama shi ne a ranar 18 ga watan Yulin tare da makamai da dama irin su alburusai da bindiga ƙirar AK-47 da sauran su.”
Sanarwar ta ce a yayin samamen da ya kai ga nasarar kama Mati Bagio, an kuma samu wata motar sata kirar Toyota Prado SUV da babura biyu.