Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba.
Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin.
- WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya
- Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi
Babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin.
Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira miliyan 700 zuwa asusun ƙananan hukumomin domin biyan albashin, a wani yanayi da ake buƙatar Naira miliyan 778 domin biyan ma’aikata albashi.
Gwamnatin ta yi nuni da cewa, Jihar Kano da ke da ƙananan hukumomi 44 na da ma’aikata dubu 30,000 ne kawai, amma Borno da ke da 27 na da ma’aikatan ƙananan hukumomi da yawansu ya kai dubu 90,000.