Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki.
Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
- Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina
- Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA
Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya.
“Na bayar da umarnin haramta sayar da da man fetur a garuruwan Bama da Banki da kuma wasu sassa na karamar hukumar Bama nan take,” in ji gwamna Zulum.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana saɓa umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.
“Babu wanda doka za ta ƙyale, sannan babu shafaffe da mai – za mu hukunta ko waye.
Gwamnan ya bai wa hukumomin tsaro damar kama duk wani gidan mai ko kuma mutum da ya take wannan umarnin.
Ya ƙara nanata zimmar da gwamnatinsa ke yi na dawo da zaman lafiya ma ɗorewa a jihar, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba da haɗin-kai a yaƙi da ƴan ta-da ƙayar baya da ake ci gaba da yi.