Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya.
Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye.
- Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina
- DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen ƙaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u.
Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.
“Na yi farin ciki da sanin cewa jami’an soji suna wajen nan, musamman sojoji, ‘yan sanda, da sauran su, domin yawancin waɗannan ayyukan wa ke yin su?
“Wasu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da fararen hula.
“Don haka, bai kamata a ƙi sukar kowane ɓangare ba a cikin wannan lamarin idan har muna son babban birnin Maiduguri da kuma jihar ta kawar da ta’addanci da sauran laifuka,” in ji Zulum.
A takaitaccen taron, Zulum ya sake kafa kwamitin tare da sake ba wa kwamitin damar kawar da duk wani nau’i na miyagun laifuka da munanan ɗabi’u a cikin birnin Maiduguri da kewaye.
Dokar hana sayar da barasa da kayan maye, a cewar gwamnan, ta samo asali ne daga yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a tsakanin ƙungiyoyin da ke gaba da juna da ƙungiyoyin asiri da karuwanci da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ‘yan fashi da sata, waɗanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya.
Gwamnan ya haɗa hannu da sojoji, ‘yan sanda, sibil difens da wasu jami’an tsaro da dama da suka haɗa da ’yan sa-kai domin shiga cikin kwamitin domin gudanar da cikakken bincike.
Da yake amincewa da aikin da ke gaban kwamitin da aka sake kafawa, shugaban kwamitin ya yi tir da tabarbarewar harkokin tsaron cikin gida a Maiduguri tare da bayyana matakin da kwamitin zai ɗauka nan take.