✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma

Bidiyon ya haifar da cece-ku-ce, amma wasu na ganin jami'an tsaron Vatican suka da tsari da ƙa'ida ba irin a Najeriya ba.

Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na cikin tawagar mahaifinsa da ta ziyarci fadar Vatican a ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo XIV.

A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya gana da Fafaroma har suka gaisa.

Amma abin da ya ja hankalin mutane shi ne lokacin da Seyi ya yi ƙoƙarin zuwa wajen mahaifinsa yayin da yake gaisawa da Fafaroma.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani jami’in tsaro ya dakatar da Seyi cikin ladabi, yana nuna masa cewa bai kamata ya matsa kusa da wajen da suke ba.

Seyi na sanye da baƙar kwat kamar yadda mahaifinsa ya sanya, ya yi ƙoƙarin isa waje shugaban ƙasa, amma jami’in tsaron ya hana shi.

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke yabawa da yadda jami’an tsaron Vatican ke aiki da tsari da ƙa’ida.

Shugaba Tinubu ya kuma gana da tsohon abokin hamayyarsa a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda ya kayar da shi a Jihar Legas a lokacin zaɓen.

Kalli bidiyon a nan ƙasa: