An tuhumi dan Ali Bongo Ondimba da wasu makusantan hambararren shugaban kasar Gabon da laifin cin amanar kasa da rashawa tare da tsare su a gidan yari, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito.
Babban dan Bongo Noureddin Bongo Valentin da tsohon mai magana da yawun shugaban kasar, Jessye Ella Ekogha, da wasu mutum hudu na kusa da hambararren shugaban, “an tuhume su tare da tsare su na wucin gadi,” in ji mai shigar da kara na Libreville Andre-Patrick Roponat.
- Zaben Gwamnan Bauchi: Bala Mohammed ya kayar da Marshal Sadique a kotu
- Kotu ta kori bukatar INEC, NNPP da Abba na korar karar APC
Bongo, mai shekara 64, wanda ya mulki kasar mai arzikin man fetur tun daga 2009, a ranar 30 ga watan Agusta ne shugabannin sojoji suka hambarar da mulkinsa, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Sakamakon da ’yan adawa da sojoji suka yi wa juyin mulkin sun bayyana cewa damfara ne, wadanda kuma ke zargin gwamnatinsa da cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari.
A ranar da aka yi juyin mulkin, sojoji sun kama daya daga cikin ’ya’yan Bongo, da manyan jami’an majalisar ministoci biyar da matarsa Sylvia Bongo Valentin.
Gidan talabijin na kasar ya nuna hotunan wadanda aka kama a gaban akwatuna cike da kudade da ake zargin an kwato su daga gidajensu ne.