✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Bauchi: Bala Mohammed ya kayar da Marshal Sadique a kotu

Kotu ta kori karar Air Marshal Sadique Abubakar saboda rashin kawo hujjojin da ke tabbatar da zarginsa na cewa an murde masa zaben

Kotun Zaben Gwamnan Jihar Bauchi ta kori karar Air Marshal Sadique Abubakr (murabsu) na Jam’iyyar, inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na PDP.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a P.T. Kwahar sun yi mori karar da Air Marshal Sadique, tsohon Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, ya shigar ne saboda gaza kawo hujjojin da ke tabbatar da zarginsa na cewa an yi murdiyar zabe.

Sadique ya je kotu yana kalubalantar sakamakon zaben na ranar 18 ga watan Maris ne bisa hujjar cewa an tafka yi magudi tare da saba dokar zabe a wasu rumfunan zabe a wasu kananan hukumomi 10.

Bugu da kari an an ki amfani da na’urar B-VAS wajen tantance masu zabe da kuma rikita na’urar a wasu rumfunan zaben kananan hukumomin.

Kananan hukumomin su ne: Toro, Dass, Zaki, Itas-Gadau, Alkaleri, Bauchi, Tafawa Balewa, Ningi, Dambam da kuma Ganjuwa.

Sai dai a yayin da yake sanar da hukuncin, alkalin ya ce hujjojin da shaidun mai kara suka gabatr na shaci-fadi ne, saboda ba sa rumfunan zaben a lokacin da abin da suke zargi ya faru, “kuma sun kasa tabbatar da cewa dan takarar APC ne ya lashe zabe,” a wuraren.

Alkali Kwahar ya kara da cewa masu karar sun kuma gaza kawo hujjojin da ke nuna cewa an sauya ainihin sakamakon zaben da suka yi zargi.