✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna ƙoƙarin shawo kan ƙarancin ruwan sha a Bauchi — Kwamishinan Ruwa

Gwamnatin Bauchi da Bankin Duniya sun kashe naira biliyan 23 da miliyan 500 a cikin watan Mayun 2022 domin magance matsalar ƙarancin ruwa.

Gwamnatin Jihar Bauchi da haɗin gwiwar Bankin Duniya sun yi aikin samar da ruwan sha a Jihar Bauchi inda suka kashe Naira biliyan 23 da miliyan 500 a cikin watan Mayun 2022, kimanin shekara biyu da suka gabata.

Ayyukan da suka gudanar sun haɗa da faɗaɗa hanyoyin rarraba ruwan a birnin Bauchi da gyara matatar ruwan da madatsar ruwan da kuma inganta bututun rarraba ruwan zuwa gidajen jama’a da sauransu.

Yayin da al’umma da gwamnati  ke murnar an warware matsalar ƙarancin ruwan sha a birnin, sai ga shi ana samun matsalar ƙarancin ruwan sha a cikin garin Bauchi.

Magidanta da dama da suka  zanta da wakilanmu sun ce, yanzu lamarin ƙarancin ruwa ya dawo, inda ’yan ga-ruwa suke sayar wa al’umma jarka ɗaya daga Naira 100, ita kuma ɗaya Naira 800 ko fiye, gwargwadon nisan inda za su kai ruwan ko daga inda suka ɗauko shi.

Wannan matsala ta yi tsanani ne sakamakon katsewar ruwan famfo da aka shafe kwana da kwanaki ba a kawowa da kuma lokacin rani da ya jawo ƙafewar rijiyoyi a unguwanni.

Dama wasu mutanen unguwanni da ke da hali sun tona rijiyoyin burtsatse da ake zargin sun janye ruwan da ke zuwa rijiyoyi, lamarin da ya damu gwamnati da al’umma.

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa gwamnati na ɗaukar matakan shawo kan lamarin, inda tuni aka fara samun ruwan famfo a wasu wuraren amma ba ya zuwa da ƙarfi.

A Unguwar Rijiyan Bauchi, ’yan ga-ruwa fiye da 50 ne ke taruwa su da sauran al’umma tun da Asuba domin su samu su jawo ruwan da za su sayar ko su yi amfani da shi.

Haka lamarin yake a wasu unguwannin Magaji Kwatas, Madina Kwatas, Unguwar Sarakuna, Unguwar Bauchi, Ibo Kwatas, Kobi, Jahun da Ƙofar Nasarawa.

Mazauna Unguwar Magaji Kwatas da Madina Kwatas sun shaida wa wakilinmu cewa, kusan kwana suke yi suna jigilar ɗiban ruwa a rijiyar tuƙa-tuƙa da ke unguwar yayin da wasu daga cikinsu ke jira a kawo wuta don su ɗiba a gidajen da ke da rijiyoyin burtsatse a unguwar.

Ba ’yan ga-ruwa kawai ba, hatta yara da matasa da magidanta kan kwashe tsawon awoyi suna bin layi domin su samo ruwan da za su kai gidajensu, wasu ma tun daga talatainin dare tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 4:00 suke fara kama layi.

Da wakilinmu ya tuntuɓi Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Bauchi Alhaji Abdulrazaƙ Nuhu Zaki dangane da wannan matsala, ya bai wa al’ummar jihar musamman na garin Bauchi haƙuri saboda wannan hali da suke ciki.

Alhaji Abdurrazaƙ Zaki ya ce, abin da ya jawo matsala har ta yi muni shi ne matasalar wutar lantarki, inda rashin samun wutar yadda ya kamata ya jawo ba wai ma’aikatar kawai ba har gidajen al’umma abin ya shafa.

Ya ce baicin wannan matsala dukkan injuna da sauran nau’rorin rarraba ruwan sha ga suna da kyau da aminci.

Ya ce, matsalar da aka fara samu ita ce daga ƙaramar tashar da aka ɗauko wutar da ke bai wamadatsar ruwa ta Gubi, wadda ta samu matsala a babban layin da ya ɗauko wutar daga Zango.

Hakan ya faru ne saboda akwai waɗansu manyan mutane da suka ɗauko wutarsu kan wannan layin da ke kai wuta ga madatsar ruwar a Gubi.

“Wannan ne ya jawo tsaiko saboda wutar da ke isa madatsar ruwan ba ta da ƙarfin da za ta juya injunan da ke rarraba ruwan ga al’umma,” in ji Kwamishinan.

Ya ƙara da cewa, Jihar Bauchi tana samun wutar lantarki ta hanyoyi biyu ne daga Jos da Gombe.

Ya ce, “Ana samun matsala sosai a dalilin rashin ƙarfin wutar, wadda ba ta iya ɗaukar injiunan ba da ruwan.

“Kodayake layin Gombe na da ƙarfi kuma yana iya juya uku daga cikin injuna biyar da muke da su, babbar matsalar, wutar layin Jos ba ta iya juya injuna biyu. Don haka rarraba ruwan ke bai wa injunan wahala sai suka riƙa kashe kansu.

“Kuma saboda yawan kashe kansu da suke yi ya sa ruwa baya iya zuwa manyan rumbunan tara ruwa biyu da muke da su a bayan otel na Zaranda da wanda ke kan Dutsin Warinje.”

Malam Nuhu Zaki ya ce matakan da ma’aikatarsa ke ɗauka ana samun nasara don yanzu ana samun ruwan sha a gidaje na wasu sa’o’i, kuma gwamnati na ƙoƙarin warware matsalar baki ɗaya saboda haka al’umma su ƙara haƙuri.