✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori karar APC kan haramcin takarar Abba

Alkalan suna karanta hukuncin ne daga wani wuri, lauyoyin bangarorin da ke shari'ar kuma suna zaune a cikin kotun suna kallon su ta majigi

Kotun Sauraron Zaben Gwamnan Jihar Kano, ta kori karar da Jam’iyyar APC da dan takararta na gwamnan Jihar Knao, Nasiru Yusuf Gawuan suka shigar gabanta na kalubalantar halascin takarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zabe da ya gabata.

Kotun ta sanar da cewa batun takara al’amari ne na cikin jam’iyya, don haka bai shafi masu kara ba, ballantana su tsoma baki a ciki.

APC da Gawuna na korafin cewa Abba ba cikakken dan jam’iyyar NNPP ba ne, kuma ba ya cikin rajistarta a lokacin da ta tsayar da shi takara, don haka bai halasta ya yi takara ba.

Daya abin da suke korafi a kai shi ne magaudin zabe da ya shafi kuri’u 130,000 wanda a cewarsu, idan aka soke, Gawuna ne zai samu galaba a zaben.

Ana karanta hukuncin Zaben Gwamnan Kano ta ‘Zoom’

Kotun da ke yanke hukunci kan zaben Gwamnan Kano ta fara karanta hukuncinta ta intanet ta manhajar Zoom.

Alkalan suna karanta hukuncin ne daga wani wuri, ba su halarci zaman kotun da kansu ba, a yayin a lauyoyin bangarorin da ke shari’ar suke zaune a cikin kotun suna kallon su ta majigi.

Ba a bayyana dalilin rashin zuwa alkalan ba a hukumance, amma wata babbar majiyar tsaro ta shaida wakilinmu a kotun cewa an yi hakan ne saboda dalilan tsaro,

Gabanin sanya ranar yanke hukuncin, an yi ta tayar a jijiyoyin wuya tsakanin jam’iyyar adawa ta APC da kuma NNPP da ke mulkin Jihar Kano.

Ga shi k uma babbar alƙalin kotun ta koka bisa yunƙurin bai wa kotun cin hanci.

Ana iya tunawa a baya-bayan nan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallami wani kwamishinansa kan zargin barazanar kisa ga alkalan kotun saboda zargin neman ba su da rashawa domin su murde shari’ar.