Darakta-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana cewa hukumar ta aikawa Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024.
Sanarwar da kakakin hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar ta ce, duk da cewa mutane 3,110 sun biya kuɗin aikin hajjinsu, yawancinsu suna jiran bizarsu daga Hukumar NAHCON.
- Ruwan sama ya lalata gidaje 200 da makarantu a Filato
- Tsadar Siminti: Majalisa ta ba Dangote da BUA wa’adi su bayyana a gabanta
Danbappa ya kuma buƙaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafi ranar da za a rufe yin bizar.
Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Kano na kammala gyara sansanin alhazai kafin a fara jigilar maniyyata.
Darakta-Janar din ya ƙara da cewa, “ba kamar shekarar da ta gabata ba, a wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake buƙata a sansanin alhazai gabanin gudanar da aikin Hajji domin amfanin maniyyata.”
Da take jawabi, Hajiya Rabi D’nyako Jami’ar gudanarwa a ofishin NAHCON da ke Kano, ta bayyana ƙudurinta na magance ƙorafe-ƙorafen biza.