✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gamsu da yadda jama’a suka fito zaɓe — Gwamna Inuwa

Akwai matakin zuwa kotu don neman haƙƙi idan akwai wanda yake ganin bai gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen ba.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya bayyana gamsuwarsa kan yadda Jama’a suka fito sosai suka kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a wannan Asabar.

Inuwa Yahaya, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa da misalin ƙarfe 11 na safiya a rumfar zaɓensa mai lamba AYU 010 da ke harabar Sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke unguwar Jekadafari a jihar.

Ya ce, fitowar jama’ar bai ba shi mamaki ba domin hakan na da nasaba ne da irin ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa.

Gwamna Inuwa, ya kuma ce akwai mataki na gaba na zuwa kotu don neman haƙƙi idan akwai wanda yake ganin bai gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen ba.

Kazalika, ya yi kira ga jama’a da cewa a taru a mara bayan ga duk wanda ya ci zaɓe domin samun damar ya iya sauke nauyin da aka ɗora masa.

Gwamnan ya ce muddin ba a bai wa zaɓaɓɓu haɗin kai ba, ba yadda za a yi su samu damar gudanar da ayyuka irin na siyasa.

Aminiya ta zaga wasu mazaɓu a ƙwaryar garin Gombe inda ta duba yadda jama’a suka fito suka yi zaɓe sabanin yadda ake tunanin cewa ba za a fito ba.