’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin yi wa matarsa kisan gilla a Jihar Adamawa.
Rundunar ’yan sandan jihar ya ce mutumin dan shekara 40 dan asalin garin Bode da ke karamar hukumar Shelleng na jihar ne.
Ana zargin bayan ya kashe matar mai suna Godiya Akwale, sannan ya kulle gawarta a cikin gidansu kafin ya tsere zuwa Jihar Ondo.
Ma’auratan sun yi aure sama da shekara uku.
- An ceto Dalibar Chibok da ciki da ’ya’ya 3 a Borno
- Ba mu sami umarnin kotu kan dakatar da Ganduje ba —APC
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar wa Aminiya kama wanda ake zargin.
Ya bada tabbacin za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.