✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto Dalibar Chibok da ciki da ’ya’ya 3 a Borno

An ce Lydia Simon da 'ya'yanta uku da kuma tsohon ciki bayan shafe shekaru 10 a hannun mayakan Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta ceto karin wata dalibar makarantar ’yan mata ta Chibok, Lydia Simon, shekara 10 bayan kungiyar Boko Haram ta sace su a makarantar.

Rahoton na cewa, a halin yanzu, Lydia, wadda ta mika wuya ga sojojin a yankin Ngoshe da ke Karamar Hukumar Gwoza, na dauke da ciki wata biyar kuma ta yi ikirarin cewa ita ’yar garin Pemi ne da ke yankin Chibok.

Dakarun Bataliya ta 82 ta Task Force da ke karamar hukumar Gwoza sun ceto Lydia Simon ne tare da ’ya’yanta uku a ranar Laraba 17 ga Afrilu, 2024.

Lydia mai lamba 68 a cikin jerin daliban da aka sace ta tsere ne daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara inda aka yi garkuwa da ita da sauran ’yan uwanta.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka cika shekaru 10 da Boko Haram ta sace dalibai mata 276 daga makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno.

Yayin da 57 daga cikinsu suka kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, daga baya kuma an kubutar da 16, yayin da aka sako 107 a lokuta daban-daban ta hanyar tattaunawa.

Gwamnatin Tarayya da Jihar Borno da Rundunar Sojojin Najeriya sun yi alkawarin ceto sauran daliban da aka sace da har yanzu ke hannun ’yan ta’addan.