✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5

Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50…

Akalla manoma 90 ne mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka kashe a Jihar Borno cikin watani biyar da suka gabata.

A baya-bayan nan kungiyoyin biyu suka kashe manoma kimanin 50, yawancinsu ta hanyar kisan gilla, kuma har yanzu an kasa dauko gawarwakin, duk da taimakon jami’an taro, a Kamarar Hukumar Kukawa.

Mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-haren kungoyiyoyin da raunin harbi.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun nan da muke cikin na shekarar 2025.

Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu.

A gefe guda kuma, mayakan kungiyar Boko Haram da ba sa ga-maciji da ISWAP sun kai wani hari garin Baga, mai tazarar kilimita 9, inda suka yi wa masunta da manoma kisan gilla.

Wata majiya a garin na Baga ta bayyana cewa kafin harin na Boko Haram manoma da masunta da ke garin sun jima suna samun kariya daga wani shugaban ISWAP a yankin.

Majiyar ta ce, manoman, “suna da takarda daga kwamandan da ke kula da yankin Malam Karanti zuwa Dawashi, mai suna Amir Akilu, kuma sun shafe watanni a karkashin kulawarsa, inda suke biyan haraji, kafin wannan harin.”

Ta bayyana cewa mayakan Boko Haram sun yi amfani da damar tafiyar da kwamandan na ISWAP da mayakansa, wajen kaddamar da mummunan harin, saboda zargin manoman da yi wa abokan gaba leken asiri a kansu.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayayana cewa mayakan na Boko Haram sun yi musu kawanya tare da barazanar harbe duk wanda ya yi yunkurin tserewa.

Ya ce, “wasunmu sun ma riga sun fara girbin wakensu kafin aka kawo harin. Suka tara mu a wuri guda suna baraznar kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa, amma duk da haka muka zabi mu tsere maimakon mutuwar wulakanci a hannunsu.

“Ina tabbatar maka sun kashe mutane 50, yawancinsu ta hanyar yankan rago, sa’annan sun yi garkuwa da wadansu. Yanzu haka sun shiga Dawashi suna yin irin wannan kisan gillar,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu bayan ya tsira.

Kisan manoma 40 a Dumba

Wannan kisan gilla na zuwa ne kimanin wata biyar bayan makamancinsa da kuniyoyin suka yi a yankin Dumba mai nisan kilomitoci kadan daga Baga.

A ranar 10 ga watan Janairu, 2025, mayakan suka kai wa wasu manoma hari da misalin karfe uku na rana a gona.

Mayakan sun yi manoman kisan gilla bisa zargin su da hada baki da sojoji, duk kuwa da izinin noma a yankin da kungiyoyin suka ba su.

‘Mun kasa dauko gawar dan uwana’

Wani wanda aka kashe dan uwansa a harin Baga mai suna Baana, ya ce an kasa dauko gawar dan uwan nasa domin yi masa jana’iza.

Baana ya ce, “gwammayar jami’an tsaro sun zo suna kokarin ganin yadda za su shiga wurin domin dauko gawarwakin, amma abin ya gagaraw.”