✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu sami umarnin kotu kan dakatar da Ganduje ba —APC

Uwar jam'iyyar rubuta wa shugaban ’yan sanda takardar korafi kan dambarwar dakatar da Ganduje

Hedikwatar Jam’iyyar APC ta Kasa ta ce ba ta da masaniyar umarnin kotu da ke dakatar da shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje.

Mai ba jam’iyyar shawara ta fuskar shari’a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce ba su sami umarnin Babbar Kotun Jihar Kano kan shugaban jam’iyyar, wanda shugabannin mazabarsa suka dakatar ba.

Ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Laraba cewa, “mun ji dai ana magana kan umarnin kotun, amma dai bai zo hannunmu ba.

“Wadanda suka dakatar da shi ba mambobin jam’iyyar APC ba ne, kuma ba sa cikin jagororinta ba ne a Jihar Kano. Ba mu san su ba,” in ji Farfesa Kana.

Ya ci gaba da cewa, “Shugabancin jam’iyyarmu ya riga ya rubuta wa shugaban ’yan sanda takardar korafi kan lamarin.”